Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yan Bindiga Sun Kuma Kai farmaki a babbn brinin Tarayya Garin Abuja, Sun Yi nasarar tafiya da Mutum hudu (4)
‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Farmaki Abuja Tare Da Sace Mutum 5.
Wasu ‘yan bindiga a ranar Litinin da daddare, sun kai farmaki kan al’ummar unguwar Bmuko a Dutse Baupma a karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya Abuja, inda suka yi garkuwa da wasu mutane hudu.
Wani mazaunin unguwar, Isah, ya ce an kai farmakin ne da misalin karfe 11:50 na dare a gidan wani Injiniya Patrick, wanda matarsa da dan uwansa na cikin wadanda aka yi garkuwa da su.
Gwamnati Na Buƙatar Dala Biliyan 10 Don Farfaɗo Da Ɓangaren Wutar Lantarki
Mamu Ya Nemi A Dauke Shi A Hannun DSS Zuwa Gidan Gyara Hali Na Kuje.
A cewarsa, masu garkuwa da mutanen, wadanda adadinsu ya kai 30, sun kai farmaki yankin Zone C, Road 5 na al’ummar yankin, inda suka yi ta harbe-harbe a sama kafin su kutsa kai gidan Injiniyan, inda suka yi awon gaba da biyu daga cikin iyalansa.
Daya daga cikin shugabannin al’umma a yankin da ya so a sakaya sunansa, ya ce, sun ji karar harbe-harbe na ‘yan mintuna kafin karfe 12 na dare, a lokacin ne daya daga cikin masu gida da ke zaune a yankin, ya aika wa masu zaman haya a gidansa sakon murya ta shafin sada zumunta cewa, an kai musu hari.
إرسال تعليق