Inalillahi! 'Yan Bindiga Sun Kashe Sarkin Gubir A Sokoto.

'Yan bindiga sun kashe Sarkin Gobir Isa Bawa bayan garkuwa da shi.

Bayanan hoto,Mako uku kenan bayan 'yan bindigar sun sace sarkin a kan hanyarsa ta komawa gida

Rahotannin da muke samu daga jihar Sokoto na cewa ƴan bindigar da suka yi garkuwa da Sarkin Gobir na garin Gatawa, Alhaji Isa Bawa, sun kashe shi.

A cikin wannan makon ne sarkin ya fito a wani bidiyo yana neman gwamnatin jihar Sokoto ta biya 'yan bindigar kudin fansa da suka bukata, inda ya ce idan wa'adi ya cika ba a biya ba za su halaka shi.

Mako uku da suka wuce ne 'yan bindiga suka yi garkuwa da sarkin a yankin kwanar maharba lokacin da yake kan hanya bayan halartar wani taro a cikin garin Sokoto.

Post a Comment

أحدث أقدم