Muhimman Abu Buwan Da Yakamata Ku Sani Akan Sabuwar Mai Shari'ar Nigeria.

Abin Da Ya Kamata Ku Sani Kan Sabuwar Babbar Mai Shari'a Ta Najeriya.

Hukumar Shari'a ta Najeriya ce ta miƙa sunan Mai shari'a Kudirat Motonmori Kekere-Ekun ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu domin ya amince tare da naɗa ta a matsayin sabuwar Alƙaliyar Alƙalan Najeriya.

A ranar Juma'a ake sa ran shugaban ƙasar zai naɗa ta a fadarsa da ke Abuja. Kakakin hukumar, Soji Oye ya ce hukumar NJC ta amince da matakin ne a zamanta wanda Babban mai shari'a na Najeriya mai barin gado, Olukayode Ariwoola ya jagoranta.

"Wannan yana da muhimmanci sosai kasancewar shekarun ajiye aiki na Mai shari'a Olukayode Ariwoola sun cika ne a ranar Alhamis 22 ga Agustan 2024." Olukayode Ariwoola ya yi riƙe matsayin ne tun daga ranar 21 ga watan Satumban shekara ta 2022, zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

'Dole a yi gyara a bangaren shari’a ta Nijeriya ' 28 Nuwamba 2023. Abu 10 kan sabon Alkalin Alkalan Najeriya27 Yuni 2022. Masu jiran a zartar musu da hukuncin kisa na ƙaruwa a Najeriya19 Aprilu 2023.

A hukumace, ya bar aiki ne a 22 ga Agusta lokacin da ya kai ritaya saboda ya kai shekara 70. A ƙa'idar Kotun Ƙolin, babban alƙali mai biye da shi ne zai maye gurbinsa.

Yanzu haka akwai alƙalai 21 a Kotun Ƙolin.

Idan Tinubu ya rantsar da ita, Mai shari'a Kekere-Ekun za ta zama mace ta biyu da ta zama Alƙaliyar Alƙalai bayan Mai shari'a Aloma Mukhtar, wadda ta riƙe matsayin tsakanin Yulin 2012 zuwa Nuwamban 2014.

Haka kuma hukumar ta amince tare da miƙa sunan mutum 27 domin zama alƙalan manyan kotunan jihohi da kuma waɗanda za su zama Kadi na kotun shari'a ta Abuja zuwa ga gwamnnoni da kuma Shugaban Ƙasa."

Wace Ce Mai Shari'a Kudirat Kekere-Ekun?

Mai shari'a Kudirat Motonmori Olatokunbo Kekere-Ekun tana ɗaya daga cikin manyan mata alƙalai na Kotun Ƙolin Najeriya. An haife ta ne a ranar 7 ga Mayun 1958. Yanzu tana da shekara 66 ke nan.

Mai shari'a Kekere-Ekun ta yi digirinta na farko a ɓangaren shari'a ne a Jami'ar Lagos, sannan ta zama ƙwararriyar lauya a 1981. Ta yi digirinta na biyu a London School of Economic and Political Science a watan Nuwamban 1983.

Ta fara aiki ne a Jihar Legas da ke Kudu maso Yammacin Najeriya. Ta zama babbar majistare a Jihar Legas a Disamban 1989. Sannan ta zama babbar alƙaliyar Babbar Kotun Legas a Yulin 1996. Ta taɓa zama Shugabar kotu ta musamman a kan sata da ƙananan makamai na shiyya ta biyu a Legas daga Nuwamban 1996 zuwa Mayun 1999.

Sannan a 22 ga Satumban 2004, sai ta koma Kotun Ɗaukaka Ƙara da aiki. Daga nan ne ta koma Kotun Ƙoli da aiki a 8 ga Yunin 2013. Bayan aikinta, tana sha'awar karatu, waƙoƙi, fasahar zamani da bayar da shawarwari.

Alkalan Najeriya na baya:

Mai Shari'a Stafford Foster Sutton: 1955-1958

Mai Shari'a Adetokunbo Ademola: 1958-1972

Mai Shari'a Taslim Olawale Elias: 1972–1975

Mai Shari'aDarnley Arthur Alexander: 1975–1979

Mai Shari'a Atanda Fatai-Williams: 1979- 1983

Mai Shari'a George Sodeinde Sowemimo: 1983–1985

Mai Shari'a Ayo Gabriel lrikefe: 1985–1987

Mai Shari'a Muhammed Bello: 1987–1995

Mai Shari'a Muhammadu Lawal Uwais: 1995–2006

Mai Shari'a Salisu Modibo Alfa Belgore: 2006–2007

Mai Shari'a Idris Legbo Kutigi: 2007–2009

Mai Shari'a Aloysius Iyorgyer Katsina-Alu: 2009–2011

Mai Shari'a Dahiru Musdapher: 2011–2012

Mai Shari'a Aloma Mariam Mukhtar: 2012–2014

Mai Shari'a Mahmud Mohammed: 2014–2016

Mai Shari'a W. S. Nkanu Onnoghen: 2016- 2019

Mai Shari'a Ibrahim Tanko Muhammed: 2019-2022

Mai Shari'a Olukayode Ariwoola: 2022 - 2024.

Post a Comment

أحدث أقدم