Da Domi-Dumi: Ana Zargin Isra'ila Da Laifukan Yaƙi Bayan Kisan Yaro Bafalasɗine

 

Da Domi-Dumi: Ana Zargin Isra'ila Da Laifukan Yaƙi Bayan Kisan Yaro Bafalasɗine

An kashe Adam ɗan shekara takwas ne lokacin da yake ƙoƙarin guje wa motocin yaƙin Isra'ila.

Bayanan hoto,An kashe Adam ɗan shekara takwas ne lokacin da yake ƙoƙarin guje wa motocin yaƙin Isra'ila.



Da safiyar ranar 29 ga watan Nuwamban bara, wasu yara Falasɗinawa suka arce a guje daga wani wuri da suke wasa a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

Mintuna kaɗan bayan haka, biyu daga cikinsu - Basil mai shekara 15 da Adam ɗan shekara takwas - suka faɗi a mace sanadiyyar harbi daga sojojin Isra'ila.




A wani ɓangare na binciken da BBC ke yi kan ayyukan sojojin Isra'ila a Gaɓar Yamma, wanda ke ƙarƙashin mamayen Isra'ilar na tsawon kimanin shekara 50, mun tattara bayanai kan abubuwan da suka faru a ranar da aka kashe yaran biyu.



Bidiyon da aka ɗauka da wayar hannu da kuma na kyamarar tsaro, da bayanan ayyukan sojojin Isra'ila a lokacin, da bayanai daga shaidu, da nazari kan wurin da lamarin ya faru, duk sun haɗu sun nuna ƙwaƙƙwarar shaidar an samu mummunan take haƙƙin bil'adama.

Post a Comment

Previous Post Next Post