Yanzu-Yanzu: Kamfanin Sadarwa Na MTN Ya Rufe Ofisoshin Sa Dake Nigeria.

Kamfanin Sadarwa Na MTN Ya Rufe Ofisoshinsa Da ke Faɗin Najeriya A Yau Talata.

Matakin kamfanin ba ya rasa nasaba da yadda wasu abokanan hulɗarsa da aka rufewa layin waya suka yi cincirindo a ofisoshin kamfanin har ma wasu suka yi ƙoƙarin kutsa kai don neman a buɗe masu layukan nasu.

MTN ya rufe layukan mutane saboda sun gaza haɗa lambarsu ta ɗan ƙasa da layinsu.

MTN ya wallafa sanarwar rufe ofisoshin nasa a shafinsa na X inda ya ce "ku sani cewa ofisoshinmu a faɗin Najeriya za su kasance a rufe yau 30 ga watan Yulin 2024.

Comments

Popular posts from this blog

Yanzu-Yanzu: Babbar kotun koli Ta Kasa Nigeria Ta Umarci Jam'iyyar PDP Ta Bai wa Tsohon Gwamnan Jigawa Daman Fitowa Takarar Shugabanci Jam'iyyar.

Abun-Mamaki: Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Usman Bauchi /Sababbin kabarai na hausa EagleNewsHausa

Ana Wata Ga Wata: 'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mata 12.