Yanzu-Yanzu: Babbar kotun koli Ta Kasa Nigeria Ta Umarci Jam'iyyar PDP Ta Bai wa Tsohon Gwamnan Jigawa Daman Fitowa Takarar Shugabanci Jam'iyyar.
Kafofin sada zumunta da yada labarai sun ruwaito Mai Shari'a Peter Odo Lifu yace wannan babban kuskure ne PDP ta hana Sule Lamido damar sayen tikitin takarar Jam'iyyar.
Har ila yau, babban kotun ta sake umartan PDP ta dakatar da taron da za ayi ranar Asabar saboda rashin shirya wajen wallafa jadawalin taron a kan Kari) lokaci domin a sanar da 'ya'yanta kamar yadda dokar zaɓe ta tanada daya bayan daya.
Kuma an kara da cewa lallai wannan shine umarnin babban kotun Kasa na uku da ke hana Jam'iyyar PDP yin taron, wanda zai ba ta damar zaɓen sababbin shugabanni a mataki na ƙasa.
A ra'ayina wannan sam bai dace ba a hana sule lamido neman tikitin neman kujerar shugaban Jam'iyyar PDP. Saboda da shima dan kasa ne yana da damar Yafito takarar a kowacce Jam'iyyar yake so.

Comments
Post a Comment