Muhimman Abu Buwan Da Yakamata Ku Sani Akan Sabuwar Mai Shari'ar Nigeria.
Abin Da Ya Kamata Ku Sani Kan Sabuwar Babbar Mai Shari'a Ta Najeriya. Hukumar Shari'a ta Najeriya ce ta miƙa sunan Mai shari'a Kudirat Motonmori Kekere-Ekun ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu domin ya amince tare da naɗa ta a matsayin sabuwar Alƙaliyar Alƙalan Najeriya. A ranar Juma'a ake sa ran shugaban ƙasar zai naɗa ta a fadarsa da ke Abuja. Kakakin hukumar, Soji Oye ya ce hukumar NJC ta amince da matakin ne a zamanta wanda Babban mai shari'a na Najeriya mai barin gado, Olukayode Ariwoola ya jagoranta. "Wannan yana da muhimmanci sosai kasancewar shekarun ajiye aiki na Mai shari'a Olukayode Ariwoola sun cika ne a ranar Alhamis 22 ga Agustan 2024." Olukayode Ariwoola ya yi riƙe matsayin ne tun daga ranar 21 ga watan Satumban shekara ta 2022, zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari. 'Dole a yi gyara a bangaren shari’a ta Nijeriya ' 28 Nuwamba 2023. A bu 10 kan sabon Alkalin Alkalan Najeriya27 Yuni 2022. Masu jiran a zartar musu da hukuncin kis...