Posts

Showing posts from February, 2025

Turkashi! Yadda Ta Kaya Tsakanin El-Rufai Da Uba Sani

Image
" Ka Yi Mubaya'a," Sanatan Da El Rufa'i Ya Tsinewa Ya Ce Tsohon Gwamna Ya Daina Ja da Uba Sani.  Hunkuyi ya shawarci tsohon gwamna Nasir El-Rufai da ya amince da Gwamna Uba Sani a matsayin sabon jagora a Kaduna. Hunkuyi ya bukaci El-Rufa’i da ya nemi gafarar Allah da kuma bai wa mutanen Kaduna hakuri kan abubuwan da ake zarginsa da aikatawa.  Hunkuyi ya kuma shawarci El-Rufa’i da ya nemi gafarar shugabannin jam’iyyar APC da ya taba bayyana su a matsayin jahilai da yake kan mulki.

Inalillahi: Mutanen Sama Da Goma Sun Mutu A Hatsarin Mota A Kano

Image
Haɗarin Babbar Mota Yayi Sanadiyyar Mutuwar Mutane Goma Sha Shida (16) A Jihar Kano. Wani hatsarin babbar mota da ya auku a birnin Kano ya yi ajalin mutum 16. Cikin wata sanarwar da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar kiyaye aukuwar hadurra ta jihar Kano, Abdullahi Labaran ya fitar, ya ce hatsarin ya auku ne ranar Alhamis da daddare a kan babbar gadar Muhammadu Buhari da ke unguwar Hotoro. Abdullahi Labaran ya ce lamarin ya faru sakamakon gudu da direban motar ke yi, lamarin da ya sa ta ƙwace masa a daidai gadar. Ya ƙara da cewa hatsarin ya rutsa da mutum 71 da motar ke ɗauke da su yayin da mutum 52 suka samu raunuka, mutum 16 kuma suka mutu,

Yanzu-Ynazu: Israela Ta Gar Gadi Hamas Da Ta Saki Israelawan Da TA Kama

Image
Isra'ila Tace Dole Hamas Ta Saki Isra'ilawa Uku Masu Rai A Ranar Asabar. Isra'ila ta ce dole ne Hamas ta saki aƙalla Isra'ilawa uku masu rai a ranar Asabar idan har ana so a ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar. Mai magana da yawun ƙasar, David Mercer ne ya bayyana hakan, bayan Hamas ta sanar da sakin Isra'ilawa uku a ranar Asabar ɗin. Tun da farko ƙungiyar ta ce za ta dakatar da sakin Isra'ilawan, bayan da ta zargi Isra'ila da karya sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wutar, saboda hana shigar da kayan buƙatu zuwa Gaza.

Tashin Hankali! Mahaifiya Ta Saysr Da Jariri Sabon Haihuwa

Image
Mahaifiya Ta Sayar da Jaririnta Mai Kwanaki 11 da Haihuwa. Rahotanni sun nuna cewa ’yan sanda sun cafke wata mahaifiya da wasu mata da ke da hannu a sayar da jariri ɗan kwanaki 11 a Jihar Delta.  Mahaifiyar jaririn ta ce an yaudareta ta sayar da ɗanta kan N600,000 yayin da wasu suka sayar da shi a kan Naira miliyan 4.  Bayan samun nasarar kama matan, rundunar ’yan sanda ta ce za ta tashi tsaye domin dakile aika-aikar fataucin jarirai a jihar Delta.

Da Dumi-Dumi: Gwamnan Abba Ya Ranatsar Da Sabon Sakatarn Shi.

Image
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya Ranatsa Da Sabon Sakataren Gwamnatin Kano. Gwamnan kano Abba Kabir Yusuf ya ranastar da Umar Farouk Ibrahim a matsayin sabon sakataren gwamantin jihar. An dai gudanar da rantsarwar ne a ofishin gwamanan na Kano, a wani kwarya kwaryar bikin rantsar da shi, yayin da kwamishinan shari'a na Kano Bar. Haruna Isa Dederi ya bashi rantsuwar kama aikin. Jaridar Dailytrust ta rawaito cewar an bashi mukamin ne bayan sauke tsohon sakatren gwamantin jihar Dr Abdullahi Baffa Bichi, da wasu kwamishinoni 5 da shugaban ma'aikatan fadar gwamanan.

Wata Sabuwa: Rikici Ya Barke Tsakanin Najaatu Da Nuhu Ribado

Image
Bidiyon Naja'atu: Ribadu Ya Dauki Zafi, Ya ba Hajiyar Wa'adi kan Bata Masa Suna.   Mai ba da shawara kan tsaro na kasa, Malam Nuhu Ribadu, ya bukaci Hajiya Naja’atu Muhammad ta janye kalamanta a bidiyon TikTok da ta yi A cikin bidiyon.   Hajiya Naja’atu ta zargi Ribadu da goyon bayan gwamnatin Tinubu, wanda a baya ya soka a lokacin da yake shugaban EFCC Lauyan Ribadu ya ce ya kamata Hajiya Naja’atu ta janye maganganunta kuma ta bayar da hakuri a jaridu guda biyar cikin kwanaki bakwai .

Yanzu-Ynazu: 'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Sama Da Dari

Image
' Yan Bindiga Sun Shiga Gari Gari, Sun Kashe Bayin Allah Duk Da Gwamna Ya Yi Sulhu da Su. Ƴan bindiga sun afkawa mutane a wasu kauyuka da ke ƙaramar hukumar Kauru a jihar Kaduna ranar Litinin, sun kashe mutum nan take Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kuma jikkata wasu. sannan suka yi awon gaɓa da mutane biyar zuwa wurin da ba a sani ba Wani mazaunin yankin ya yi kira ga gwamnati ta gaggauta ɗaukar matakan kare su daga sharrin waɗannan maharan da ba su da tausayi. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi! Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum Kaduna -  Miyagun 'yan bindiga sun afkwa mutane a kauyen Kumana da ke yankin gundumar Kwassam da kuma Rumaya a ƙaramar hukumar Kauru ta jihar Kaduna. 

Inalillahi! Anyi Wa Mutane Kasar Sudan Mummunan Kisa

Image
Daru Ruwan Mutanen Da Aka kashe A Kasar Sudan. An kashe gomman fararen hula a Sudan yayin da ake cigaba da gwabza yaƙi tsakanin sojoji da dakarun RSF. Rahotanni sun bayyana cewa harin saman da ake zargin sojoji sun kai ranar Litinin a wuraren da ke ƙarƙashin ikon RSF a birnin Nyara da ke kudancin Darfur, ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla fararen hula 30. A gefe guda kuma ana ganin fiye da fararen hula 60 ne suka mutu bayan dakarun RSF sun harba manyan makamai a birnin el Fasher.

Kyrgyzstan Ta Hana Mata Sanya Liqabi

Image
Kyrgyzstan Ta Haramta Wa Mata Sanya Niqabi. Kyrgyzstan ta zama ƙasar da Musulmi suka fi rinjaye ta baya-bayan nan a yankin tsakiyar Asiya da ta haramta amfani da lilliɓin da mata ke rufe jikinsu gaba-daya - niqabi. Dokar da ta fara aiki tun daga jiya Asabar, ta tanadi hukuncin tarar dala 230 (kuɗin ƙasar som 20,000) a kan duk matar da ta sanya niqabin a wurin jama'a ko waje na gwamnati. Gwamnatoci a ƙasashen tsakiyar Asia sun daɗe suna magana ko muhawara kan tufafin mata na Musulunci misali niqabi da kuma gemu ga maza, inda gwamnatocin da ke da tsananin aƙidar raba addini da harkar mulki suke tsoron tasirin Musulunci a ƙasashen. 'Yanmajalisar dokokin ƙasar ta Kyrgyzstan sun ce ana buƙatar dokar saboda dalilai na tsaro - ta yadda za a iya ganin fuskar mutum a kuma gane ko wace ce. To amma kuma masu suka sun ce dokar ta tauye wa mata 'yancinsu na zaɓar tufafin da suke son sanyawa. Dokar wadda Shugaba Sadyr Japarov ya sanya wa hannu ranar 21 ga watan Janairu da ya wuce, ba ta ...

Innalillahi! Ana Yin kurin Kai Hari Mummunan Ga Musulman Kudancin Nigeria.

Image
Ana Yunkurin Farmakar Musulmai A Kudancin Najeriya,' Kungiyar MURIC Ta Tona Asiri . Kungiyar MURIC ta zargi wasu kungiyoyi da shirin haddasa rikici kan batun kafa shari'ar Musulunci a Kudu maso Yamma.  A cewar MURIC, ana amfani da kafofin sada zumunta wajen tunzura jama’a da kuma yin barazana ga shugabannin Musulmi Kungiyar ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya tsawatarwa mutanensa da ke barazanar farmakar Musulamn da ke a Kudu. Abuja - Kungiyar kare hakkin Musulmai (MURIC) ta zargi wasu kungiyoyi da shirin haddasa tashin hankali ga Musulmin Kudu maso Yamma.  Kungiyar ta bukaci Sufeto Janar na ‘yan sanda, Darakta Janar na DSS da sauran jami’an tsaro su dakile yunkurin kuma su kare rayukan Musulmi.  MURIC na zargin ana shirin farmakar Musulmai MURIC ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da daraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, ya fitar a ranar Juma’a kamar yadda The Guardian ta ruwaito . 

Da Dumi-Dumi: Gwamna Zulum Yayi Tagomashi Ga Iyalan Babban Jami'in Sojan Da Aka Kashe.

Image
Gwamna Zulum Ya Tuna Da Iyalan Babban Jami'in Sojan Da 'Yan Boko Haram Suka Kashe. Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya tuna da iyalan marigayi Laftanal Kanal Thomas Alari wanda ya rasu a fagen daga. Farfesa Babagana Umara Zulum ya ba iyalan marigayin gudunmawar kuɗi N30m tare da miƙa saƙon ta'aziyyarsa a gare su. Gwamnan ya kuma ba iyalan marigayin wanda ya rasa ransa a yaƙi da ƴan Boko Haram cewa zai ci gaba da tallafa musu da na sauran sojojin da suka rasu. Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayar da gudunmuwar N30m ga iyalan marigayi Laftanar Kanal Thomas Alari.  Gwamna Zulum ya ba da gudunmawar kuɗin ne bayan marigayin ya rasa ransa a ci gaba da yaƙin da ake yi da Boko Haram a yankin Timbuktu Triangle. 

Turkashi: Tsohon Ministan Sadarwa Ya Caccaki Masu Sukur Sahri:a

Image
Akwai Jahilci': Tsohon Ministan Sadarwa A Mulkin Buhari Ya Caccaki Masu Sukar Shari'a.  Tsohon ministan sadarwa, Adebayo Shittu, ya soki masu adawa da kafa kwamitin shari'ar Musulunci a Kudu maso Yamma, yana cewa jahilci ne ke haddasa hakan.  A cewarsa, kwamitocin sun dade suna gudanar da shari’o’in addini a wasu jihohi ba tare da haddasa wata matsala ba Ya kara da cewa Musulmi suna da ’yancin gudanar da harkokinsu bisa doka ta shari'a, don haka gwamnati ba ta da ikon hana su yin hakan. Ibadan, Oyo - Tsohon ministan sadarwa, Adebayo Shittu, ya soki masu adawa da kwamitin shari'ar Musulunci a Kudu maso Yamma.  Mr. Shittu ya ce adawar da ake yi jahilci ne saboda kwamitocin sun dade suna gudanar da shari’o’i na addini a wasu jihohi ba tare da wata matsala ba. 

Da Dumi-Dumi: Adadin Mutanen Da Suka Mutu A Hatsarin Jirgin Sama

Image
'Duka Mutanen Da Ke Cikin Jirgin Da Yayi Hadari   Philadelphia Sun Mutu ' Ofishin magajin garin birnin Philadelphia ya ce duka mutanen shidan da ke cikin jirgin da ya yi hatsari a wata unguwa a birnin sun rasu. Cikin wata sanarwa da ofishin ya fitar ya mutum hudu ne a cikin jirgin sai kuma ma'aikatansa biyu. Jirgin na ɗaukar marasa lafiya da ya yi hatsari a birnin na dauke da wani karamin yaro fda mahaifiyarsa da likita da ma'aikacin jinya. Ƙaramin jirgin ɗaukar marasa lafiya ya faɗa kan rukunin gidajen al'umma a Philadelphia na ƙasar Amurka, lamarin da ya sa gidaje da motoci suka kama da wuta. Lamarin ya ji wa mutane da dama rauni duk da dai har yanzu ba a tantance ɓarnar da ta afku ba.

Yanzu-Ynazu; Izala Ta Gayyaci Tunibu Da Atiku Wani Ga Garumin Taro

Image
Izala Ta Gayyaci Tinubu, Atiku da Wasu Manya Taron Neman Naira Biliyan 1.5. Ƙungiyar Izala (JIBWIS) ƙarƙashin jagorancin Sheikh Yahaya Jingir ta gayyaci al’ummar Musulmi zuwa babban taron ƙasa da za a gudanar a Abuja Za a gudanar da taron a ranakun Asabar da Lahadi, 8 zuwa 9 ga watan Fabrairu, 2025, a Cibiyar Shehu Musa Yar’Adua da Babban Masallacin Abuja.  Kungiyar za ta kaddamar da asusun neman taimako kudi domin tallafawa harkokin ilimi da ilimantarwa da ya kai har Naira biliyan 1.5 a yayin taron. FCT, Abuja - Ƙungiyar Izala ƙarƙashin shugabancin Sheikh Yahaya Jingir, wacce ke da hedikwata a Jos, ta fitar da sanarwar gayyatar al’ummar Musulmi zuwa babban taronta na ƙasa.  Rahotanni sun bayyana cewa za a gudanar da taron ne a birnin tarayya Abuja, inda za a haɗu domin tattaunawa da bunƙasa harkokin ilimi .