Turkashi: Tsohon Ministan Sadarwa Ya Caccaki Masu Sukur Sahri:a
Akwai Jahilci': Tsohon Ministan Sadarwa A Mulkin Buhari Ya Caccaki Masu Sukar Shari'a.
Tsohon ministan sadarwa, Adebayo Shittu, ya soki masu adawa da kafa kwamitin shari'ar Musulunci a Kudu maso Yamma, yana cewa jahilci ne ke haddasa hakan.
A cewarsa, kwamitocin sun dade suna gudanar da shari’o’in addini a wasu jihohi ba tare da haddasa wata matsala ba Ya kara da cewa Musulmi suna da ’yancin gudanar da harkokinsu bisa doka ta shari'a, don haka gwamnati ba ta da ikon hana su yin hakan.
Ibadan, Oyo - Tsohon ministan sadarwa, Adebayo Shittu, ya soki masu adawa da kwamitin shari'ar Musulunci a Kudu maso Yamma.
Mr. Shittu ya ce adawar da ake yi jahilci ne saboda kwamitocin sun dade suna gudanar da shari’o’i na addini a wasu jihohi ba tare da wata matsala ba.

Comments
Post a Comment