Da Dumi-Dumi: Gwamna Zulum Yayi Tagomashi Ga Iyalan Babban Jami'in Sojan Da Aka Kashe.
Gwamna Zulum Ya Tuna Da Iyalan Babban Jami'in Sojan Da 'Yan Boko Haram Suka Kashe.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya tuna da iyalan marigayi Laftanal Kanal Thomas Alari wanda ya rasu a fagen daga.
Farfesa Babagana Umara Zulum ya ba iyalan marigayin gudunmawar kuɗi N30m tare da miƙa saƙon ta'aziyyarsa a gare su.
Gwamnan ya kuma ba iyalan marigayin wanda ya rasa ransa a yaƙi da ƴan Boko Haram cewa zai ci gaba da tallafa musu da na sauran sojojin da suka rasu.
Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayar da gudunmuwar N30m ga iyalan marigayi Laftanar Kanal Thomas Alari.
Gwamna Zulum ya ba da gudunmawar kuɗin ne bayan marigayin ya rasa ransa a ci gaba da yaƙin da ake yi da Boko Haram a yankin Timbuktu Triangle.

Comments
Post a Comment