Da Dumi-Dumi: Adadin Mutanen Da Suka Mutu A Hatsarin Jirgin Sama

'Duka Mutanen Da Ke Cikin Jirgin Da Yayi Hadari  Philadelphia Sun Mutu'

Ofishin magajin garin birnin Philadelphia ya ce duka mutanen shidan da ke cikin jirgin da ya yi hatsari a wata unguwa a birnin sun rasu.

Cikin wata sanarwa da ofishin ya fitar ya mutum hudu ne a cikin jirgin sai kuma ma'aikatansa biyu.

Jirgin na ɗaukar marasa lafiya da ya yi hatsari a birnin na dauke da wani karamin yaro fda mahaifiyarsa da likita da ma'aikacin jinya.

Ƙaramin jirgin ɗaukar marasa lafiya ya faɗa kan rukunin gidajen al'umma a Philadelphia na ƙasar Amurka, lamarin da ya sa gidaje da motoci suka kama da wuta.

Lamarin ya ji wa mutane da dama rauni duk da dai har yanzu ba a tantance ɓarnar da ta afku ba.

Comments

Popular posts from this blog

Yanzu-Yanzu: Babbar kotun koli Ta Kasa Nigeria Ta Umarci Jam'iyyar PDP Ta Bai wa Tsohon Gwamnan Jigawa Daman Fitowa Takarar Shugabanci Jam'iyyar.

Abun-Mamaki: Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Usman Bauchi /Sababbin kabarai na hausa EagleNewsHausa

Ana Wata Ga Wata: 'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mata 12.