Tashin Hankali! Mahaifiya Ta Saysr Da Jariri Sabon Haihuwa
Mahaifiya Ta Sayar da Jaririnta Mai Kwanaki 11 da Haihuwa.
Rahotanni sun nuna cewa ’yan sanda sun cafke wata mahaifiya da wasu mata da ke da hannu a sayar da jariri ɗan kwanaki 11 a Jihar Delta.
Mahaifiyar jaririn ta ce an yaudareta ta sayar da ɗanta kan N600,000 yayin da wasu suka sayar da shi a kan Naira miliyan 4.
Bayan samun nasarar kama matan, rundunar ’yan sanda ta ce za ta tashi tsaye domin dakile aika-aikar fataucin jarirai a jihar Delta.

Comments
Post a Comment