Turkashi: Wani Matashi Yayi Tur Da Masu Yin Mummunan Kalamai Ga Sheik Dahiru Usman Bauchi.


Wani Matashi Mai Suna Yusuf Sa'idu wanda akafi sani da Yusuf Senior dan garin Dogon-Dawa karamar hukumar Birnin-Gwari Kaduna state kuma dalibin jami'ar Ahmed Bello University (ABU) Zaria Ya Bayyana Cewa:


Ya kamata mu dabi'antu da dayin adalci wa junanmu a mtasayin mu na musulmai wadanda ke annabi daya kur'ani daya, alkibla daya kar mubari son zuciya ya rufe mana idanuwa. Sheik Dahiru Usman Bauchi ya kasance shahararren babban malamin addinin musulunci kuma masoyin annabi Muhammad tsantsa ba Nigeria kadai ba Africa baki daya. 


Ya sadaukar da rayuwarsa tun yana matshi baki daya wajan kiran mutane zuwa ga Allah da manzon Allah har zuwa lokacin da karfinsa ya Kare. Babban abunda ya ban mamaki wai ace musulmi zai iya zagin shehu! saboda me? Me shehu yayi masa? Ko da ma ace yayi masa wani abu na rashin kyautawa, ko bakomai ya kamata yaci arzikin musulunci, idan baici arzikin kasancewan shi kahdimul isalm, ko kuma yaci arzikin imimin sa, malintar sa, tsufar sa ko kuma 'ya'yan sa amma ace ko daya bai samu ba. 


Masu saurare shin Kuna tunanin cewa musulmi wanda ya amsa sunansa musulmi zai iya zagin shehu? Sun manta da zance shugaba s.a.w inda yake cewa "malamai magada annabawa, wabda ya girmama su ni ya girmama, wanda ya zage su ni ya zaga".


Nasan wasu za suce marsalar shehu dan darikar sufaye ne (tijjaniyya). Ya kamata mu fara sanin me darika take nufi, darika wata hanya ce wacce take mai sauki wajen samun karin falala wajan Allah s.w.a.

Kamar nafilane ana yin ta domin Karin samun falala wajan Allah. Misali ance muyi sallah azahar raka"a hudu wajan, kai kuma sai kaga cewa kana da dama kara raka'a hudu bayan sallah haka darika take ba wani abu bane daban.


Ya kara da cewa akwai wadanda suke cewa annabi be yiba, gaskiya ne annabi be yiba. Amma ina so asani cewa annabi be yiba ba hujja bane annabi ya hana shine hujja.


Wasu kuma sunce marsalar darika sai anyi wa mutum izini, izini halas keanan duk abunda ba izini Haram ne. Misali menene bababcin zina da aure?...Izini ne. Duk abunda ba izini Haram ne.


Menene ake yi a cikin darika? Ba wani abu bako Salatin annabi, istigifari, da hailala, sune ba wani sabo a cikin. Rawar da darika take ta kawa ga musulmi: Tana taimakawa wajen tsarkake zuciya mutum daga dukkaan, tsatsa, hassada, kokonto, kyashi, rowa, girman kai, riya, guulma, munafurci da dukkan abubuwan ki.


Tana kusantar da Mutum ga annaabi Muhammad Sallalahu Alaihi Wasallam ta hanyar ya waita salati kullum ga shugaba. Kuma tana janwo arzikin ga mutum da ta hanyar ya waita istigifari da cinye zunubi fiye da yadda wuta ke cinye itace. 


Zuciya tana samun tsarki ta hanyar ya waita hailala (la'ilaha'illalahu) idan kace kace kullum sai kayi dubu goma ba zaka iya ba, saboda katakura ma kanka. Ida kuma kace kullum zakayi dari idan wata rana ka manta shikenan amma idan kana cikin darika anabinka ko da baka da lafiya idan warke sai kabuya .


Dan darika yana salati kullum 212 idan ka lissa a shekara yana da salati 76,320,yana istigifari 230 a kullum idan ka lissafa a shekara yana da istigifari 82,800, Kuma yana hailala (la'ilaha'illalahu) 300 a kullum idan ka lissafa a shekara yana da hailala 108,000. 

Wannan itace darika a takaice Allah Ubangijin yasa mudace alfarma shugaban halitta annabi Muhammadu 

Comments

Popular posts from this blog

Yanzu-Yanzu: Babbar kotun koli Ta Kasa Nigeria Ta Umarci Jam'iyyar PDP Ta Bai wa Tsohon Gwamnan Jigawa Daman Fitowa Takarar Shugabanci Jam'iyyar.

Abun-Mamaki: Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Usman Bauchi /Sababbin kabarai na hausa EagleNewsHausa

Ana Wata Ga Wata: 'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mata 12.