Inalillahi: Mutanen Sama Da Goma Sun Mutu A Hatsarin Mota A Kano

Haɗarin Babbar Mota Yayi Sanadiyyar Mutuwar Mutane Goma Sha Shida (16) A Jihar Kano.

Wani hatsarin babbar mota da ya auku a birnin Kano ya yi ajalin mutum 16.

Cikin wata sanarwar da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar kiyaye aukuwar hadurra ta jihar Kano, Abdullahi Labaran ya fitar, ya ce hatsarin ya auku ne ranar Alhamis da daddare a kan babbar gadar Muhammadu Buhari da ke unguwar Hotoro.

Abdullahi Labaran ya ce lamarin ya faru sakamakon gudu da direban motar ke yi, lamarin da ya sa ta ƙwace masa a daidai gadar.

Ya ƙara da cewa hatsarin ya rutsa da mutum 71 da motar ke ɗauke da su yayin da mutum 52 suka samu raunuka, mutum 16 kuma suka mutu,

Comments

Popular posts from this blog

Yanzu-Yanzu: Babbar kotun koli Ta Kasa Nigeria Ta Umarci Jam'iyyar PDP Ta Bai wa Tsohon Gwamnan Jigawa Daman Fitowa Takarar Shugabanci Jam'iyyar.

Abun-Mamaki: Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Usman Bauchi /Sababbin kabarai na hausa EagleNewsHausa

Ana Wata Ga Wata: 'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mata 12.