Kyrgyzstan Ta Hana Mata Sanya Liqabi

Kyrgyzstan Ta Haramta Wa Mata Sanya Niqabi.

Kyrgyzstan ta zama ƙasar da Musulmi suka fi rinjaye ta baya-bayan nan a yankin tsakiyar Asiya da ta haramta amfani da lilliɓin da mata ke rufe jikinsu gaba-daya - niqabi.

Dokar da ta fara aiki tun daga jiya Asabar, ta tanadi hukuncin tarar dala 230 (kuɗin ƙasar som 20,000) a kan duk matar da ta sanya niqabin a wurin jama'a ko waje na gwamnati.

Gwamnatoci a ƙasashen tsakiyar Asia sun daɗe suna magana ko muhawara kan tufafin mata na Musulunci misali niqabi da kuma gemu ga maza, inda gwamnatocin da ke da tsananin aƙidar raba addini da harkar mulki suke tsoron tasirin Musulunci a ƙasashen.

'Yanmajalisar dokokin ƙasar ta Kyrgyzstan sun ce ana buƙatar dokar saboda dalilai na tsaro - ta yadda za a iya ganin fuskar mutum a kuma gane ko wace ce.

To amma kuma masu suka sun ce dokar ta tauye wa mata 'yancinsu na zaɓar tufafin da suke son sanyawa.

Dokar wadda Shugaba Sadyr Japarov ya sanya wa hannu ranar 21 ga watan Janairu da ya wuce, ba ta ambaci niqab ƙarara ba, amma ta ce duk tufar da za ta sa a kasa gane mutum (saboda ya rufe fuska) a wuraren gwamnati da taruwar jama'a.

Sai dai dokar ba ta shafi rufe fuska da ake bukata saboda yanayin aiki ko dalilai na lafiya ba.

'Yanmajalisar dokoki da kuma shugabannin addini da ke da alaƙa da gwamnati sun ce haramcin bai shafi hijabi ba - wanda ke rufe kai da wuya amma ana ganin fuska.

Kyrgyzstan ita ce kasa ɗaya kawai a yankin Asiya ta Tsakiya da ba ta harmta amfani da hijabi a makarantu da ofisoshi ba.

Comments

Popular posts from this blog

Yanzu-Yanzu: Babbar kotun koli Ta Kasa Nigeria Ta Umarci Jam'iyyar PDP Ta Bai wa Tsohon Gwamnan Jigawa Daman Fitowa Takarar Shugabanci Jam'iyyar.

Abun-Mamaki: Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Usman Bauchi /Sababbin kabarai na hausa EagleNewsHausa

Ana Wata Ga Wata: 'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mata 12.