Yanzu-Ynazu; Izala Ta Gayyaci Tunibu Da Atiku Wani Ga Garumin Taro
Izala Ta Gayyaci Tinubu, Atiku da Wasu Manya Taron Neman Naira Biliyan 1.5.
Ƙungiyar Izala (JIBWIS) ƙarƙashin jagorancin Sheikh Yahaya Jingir ta gayyaci al’ummar Musulmi zuwa babban taron ƙasa da za a gudanar a Abuja Za a gudanar da taron a ranakun Asabar da Lahadi, 8 zuwa 9 ga watan Fabrairu, 2025, a Cibiyar Shehu Musa Yar’Adua da Babban Masallacin Abuja.
Kungiyar za ta kaddamar da asusun neman taimako kudi domin tallafawa harkokin ilimi da ilimantarwa da ya kai har Naira biliyan 1.5 a yayin taron.
FCT, Abuja - Ƙungiyar Izala ƙarƙashin shugabancin Sheikh Yahaya Jingir, wacce ke da hedikwata a Jos, ta fitar da sanarwar gayyatar al’ummar Musulmi zuwa babban taronta na ƙasa.
Rahotanni sun bayyana cewa za a gudanar da taron ne a birnin tarayya Abuja, inda za a haɗu domin tattaunawa da bunƙasa harkokin ilimi .

Comments
Post a Comment