Sheikh DAurawa Yayi Kira Ga Ɗaukacin Muslimai; Dasu Guji Zanga-Zanga Akan Tsadar Rayuwa.

Sheikh Aminnu Ibrahim Daurawa Ya Yi Kira Ga Musulmi Da Su Nisanci Zanga-zanga Kan Adawa Da Tsadar Rayuwa.

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan mazaunin Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su guji gudanar da zanga-zangar nuna adawa da tsadar rayuwa a fadin kasar nan.

Ana shirin gudanar da zanga-zangar na kwanaki 10 domin nuna adawa da tsadar rayuwa da kasar ke fuskanta sakamakon hauhawar farashin man fetur, hauhawar farashin kayayyakin abinci, rashin tsaro da dai sauransu.

Ma’aikatan Ruwa Na Jihar Kaduna Sun Yi Zanga-zangar Rashin Albashi. Sin Na Fatan Amurka Za Ta Martaba Ikon Mulkin Kai Tsaro Da Moriyar Ci Gabanta. Amma a hudubar da Sheikh Daurawa ya gabatar a Kano a Juma’ar da ta gabata, ya yi nuni da cewa zanga-zangar tana da illa fiye da alherinta, kuma bai kamata a karfafa mata gwiwa ba.

Ya ce, “Ba ma goyon bayan zanga-zangar saboda mun ga abin da ya faru a Siriya, Sudan, Libya da Iraki. “Wataƙila za a gudanar da zanga-zangar ne da kyakkyawan nufi amma wasu masu mugun nufi za su iya shiga ciki su bata lamarin. Dukkanmu mun san da shirin masu tayar da kayar baya na kasa da suke shiri don raba kasa. Suna da kudi da makamai. Za su yi amfani da ku a cikin wannan zanga-zangar don cimma burinsu,” inji shi.

Labarai Masu Nasaba

Farashin Abinci Zai Faɗi Warwas Nan Da Kwanaki 180 – Ministan Noma

Ku Shirya Kare Kanku Ga Hukumomin Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa – Majalisar Kaduna

 Ya ba da shawarar cewa, a maimakon yin zanga-zanga, ya kamata a nemi hanyoyin diflomasiyya da suka hada da baiwa gwamnati shawara da masu ruwa da tsaki kan matakan da suka dace don magance matsalar.

“Ba tsoro muke ji ba. Amma zanga-zanga ba ta haifar da sakamako mai kyau. Mutane sukan ƙare da rasa ɗan abin da suke da shi. Ya kamata mu ba gwamnati shawara kan abin da za ta yi maimakon haka. Amma a cikin wannan mawuyacin lokaci, ya kamata mu yi taka tsantsan da abin da muke faɗa ko aikatawa,” in ji shi.

Tags: Gwamnatin TinubuTsadar RayuwaZanga-zangar adawa da yunwa.

Post a Comment

Previous Post Next Post