Ana Wata Ga Wata: 'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mata 12.


Wannan lamari dai ya kara dagula hare-haren da kungiyoyi masu dauke da makamai ke ci gaba da kai wa a wasu jihohin arewacin kasar. Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun yi garkuwa da wasu mata 12 a gundumar Mussa da ke karamar hukumar Askira-Uba a jihar Borno. Rahotanni sun ce an dauke su ne yayin da suke dawowa daga gonakinsu da yammacin ranar Asabar. 

 Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan, Nahum Daso, ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi.

Daso ya bayyana cewa rundunar ta fara gudanar da bincike kan lamarin. Ya ce, “A jiya an yi garkuwa da wasu mata 12 da suke dawowa daga gonakinsu a Askira-Uba, wadanda ake zargin ‘yan Boko Haram ne suka yi. 


 "Har yanzu ba a fayyace cikakkun bayanai ba, amma ana kokarin," in ji PPRO. Wannan sace-sacen ya kasance na baya-bayan nan a jerin hare-haren da kungiyoyi masu dauke da makamai ke kaiwa a wasu jihohin arewacin kasar.

Comments

Popular posts from this blog

Yanzu-Yanzu: Babbar kotun koli Ta Kasa Nigeria Ta Umarci Jam'iyyar PDP Ta Bai wa Tsohon Gwamnan Jigawa Daman Fitowa Takarar Shugabanci Jam'iyyar.

Abun-Mamaki: Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Usman Bauchi /Sababbin kabarai na hausa EagleNewsHausa