Da Dumi-Dumi: Dalibai Sama Da Milyan 1 Ne Suka Ci Maki Jamb 200

Dalibai Miliyan 1.4 Da Suka Rubuta Jarra-bawar UTME Sun Ci Maki Kasa Da 200

Hukumar shirya jarabawar sharar fagen shiga manyan makarantu a kasar nan (JAMB), a ranar Litinin da ta gabata ta sake sakamakon jarabawar na shekarar 2024, inda sakamakon ya nuna cewa dalibai 1,402,490 daga cikin 1,842,464 sun kasa iya cin maki 200 daga cikin maki 400 na jarabawar.


Adadin daliban da suka kasa cin sakamakon sun dauki kaso 78 cikin dari na duk-kanin daliban da suka zauna domin rubuta jarabawar kamar yadda sakamakon da JAMB ta fitar ya nuna.. JAMB Ta Fitar Da Sakamakon Jarrabawar 2024, Sakamako 64,624 Na Karkashin Bincike.

UTME: JAMB Ta Ba Da Umurnin Kamo Iyayen Da Aka Gansu Kusa Da Cibiyoyin Zana Jarabawa Da yake bayar da bayani kan sakamakon jarabawar dalibai 1,842,464, Rajistara na hukumar, Farfesa Ishak Oloyede, ya ce, “Dalibai 8,401 ne kawai suka iya samun maki 300 ko fiye da haka, dalibai 77,070 sun ci maki 250 ko fiye, sai kuma 439,974 da suka ci maki 200 ko fiye, yayin da kuma dalibai 1,402,490 suka ci maki kasa da 200.”


Ya ce, hukumar ba ta saba wallafa sunayen wadanda suka yi zarra a jarabawar ba, illa iyaka tana fito da jerin yadda sakamakon ya kaya. A gefe guda, shugaban hukumar ya nemi al’umma da ka da su sake fadawa irin tarkon da Mmesoma ta taba jefa wasu, inda ya ce a kowani lokaci wani ko wata daliba suka yi ikirarin samun wasu sakamakon jarabawar mai gwabi, kafin mutane su dukufa wajen musu kyautuka su nemi tabbaci daga hukumar domin kauje wa shiga kokonto.


Labarai Masu Nasaba

Yadda Hanyoyin Ruwa Suka Zama Tarkunan Mutuwa A Nijeriya

Girman Darajar Manzon Allah SAW Da Allah Ya Yi Rantsuwa Da Ita (7)


 Oloyede ya kuma ce an rike sakamakon jarabawar dalibai 64,624 daga cikin wadanda suka zana jarabawar, inda ake kan gudanar da bincike kan zargin satan amsa, sahihancin cibiyar zana jarabarsu da dai sauransu. A cewarsa, adadin daliban da suka yi rajistan zana jarabawar sun kai 1,989,668, inda a cikin dalibai 80,810 ba su je sun zana jarabawar ba, “Adadin dalibai 1,904,189 ne suka zauna domin zana jarabar UTME a cikin kwanaki shida.”

Oloyede ya ce hukumar ta shirya wa daliban da suke kasashen waje jarabawa a wurare tara da suka hada da Abidjan, Ibory Coast; Addis Ababa, Ethiopia; Buea, Cameroon; Cotonou, jamhuriyyar Benin; London, Burtaniya; Jeddah, Saudi Ara-bia; da Johannesburg, Afrika ta Kudu.

Post a Comment

Previous Post Next Post