Da Dumi-Dumi: 'Ibtila'in' Da Ya Faru Da Falasɗinawa A 1948

Al-Nakba: 'Ibtila'in' Da Ya Faru Da Falasɗinawa A 1948

A kowace ranar 15 ga watan Mayu, Falasɗinawa a faɗin duniya na tunawa da ranar al-Nakba, wadda ke nufin 'bala'i'. Daga watannin ƙarshe na shekarar 1947 zuwa farko-farkon shekarar 1949, kimanin Falasɗinawa 750,000 suka zama ƴan gudun hijira, bayan tarwatsa su daga yankin da ya zama ƙasar Isra'ila. Da dama daga cikin su an kore su ne da ƙarfi da yaji, yayin da wasu suka gudu domin tsira da ransa. Ranar Al-Nakba na tunawa ne da lokacin da aka kori Falasɗinawan daga gidajensu da kuma shekarun da suka kwashe suna gudun hijira. Lokaci na zaman ɗar-ɗar kuma an samu ɓarkewar rikice-rikice tsakanin Falasɗinawa da ƴan ƙasar Isra'ila a irin wannan rana a shekarun baya. 

Ta yaya lamarin ya faru kuma me ya sa Falasɗinawa ke nuna "mabuɗin komawa"

 a irin wannan rana? . Bayanan hoto,Falasɗinawa na ɗaukar makulli a matsayin wani tambarin ƴancinsu na komawa gidajensu da suka baro Yunƙurin kafa ƙasar Isra'ila da Tawayen Larabawa.

A ƙarshe-ƙarshen ƙarni na 19, yunƙurin kafa ƙasar Yahudawa ya yi ƙarfi a yankin Turai. Wanda ya assasa manufar samar da ƙasar Yahudawa, Theodor Herzl, a shekarar 1896 ya bayyana cewa samar da ƙasar Yahudawa zai magance tsawon lokacin da aka kwashe ana karkashe Yahudawa a ƙasashen Turai saboda ƙyamar da ake yi musu. A 1917, Birtaniya, wadda ke iko da yankin Falasɗinu bayan wargajewar daular Ottoman - ta samar da wata yarjejeniya wadda aka yi wa laƙabi da 'Balfour Declaration'.

Takardar ta bayyana cewa za ta taimaka "wajen samar da wani wuri a cikin yankin Falasɗinu wanda zai zamo gida ga Yahudawa". Bayanin ya kuma ƙara da cewa kada a yi wani abu "wanda zai zamo cikas ga rayuwa da ƴancin addinin al'ummar da ba Yahudawa ba waɗanda ke zama a yankin na Falasɗinu". Dubban Yahudawa masu gudun hijira ne suka tuɗaɗa zuwa yankin na Falasɗinu domin kauce wa cin zarafi a ƙasashen Turai, musamman na gabashin Turai.

Lokacin da aka riƙa samun tuɗaɗar Yahudawa ƴan gudun hijira zuwa yankin, sai aka riƙa samun rikici tsakanin Yahudawa da Falasɗinawa tun daga shekarun 1920 zuwa 1930. Rikice-rikicen da aka samu a farko-farko sun haifar da asarar ɗaruruwan rayuka. Yahudawan da suka isa yankin sun sayi fiyalye masu yawa daga hannun manya da ƙananan manoma Larabawa. Sai dai daga baya ƙiyayya a gare su ta fara ƙamari, musamman a lokacin da suka fara neman zama a filayen gonaki da suka saya, inda suka fara fitar da Larabawa waɗanda ke zama a filayen a matsayin ƴan haya.

A shekarar 1936 Larabawa Falasɗinawa sun yi wa Turawan Birtaniya gagarumin bore - inda suka buƙaci a ba su ƴancinsu tare da kawo ƙarshen shirin tsugunar da Yahudawa a yankin da saye filaye mallakin Larabawa. Masana tarihi sun ce an kashe Larabawa 5,000 da raunata wasu 15,000 a lokacin boren, wanda ya kawo ƙarshe a 1939. Masana tarihin sun ce ɗaruruwan Turawan Birtaniya da Yahudawa sun jikkata sanadiyyar boren.


Taswirar yankin Falasɗinawa ƙarƙashin ikon Turawan Birtaniya

Bayan lafawar boren, gwamnatin Birtaniya ta fitar da wata matsaya a 1939, inda ta taƙaita tuɗaɗar Yahudawa zuwa ƙasar Falasɗinu na tsawon shekara biyar tare da kafa dokar cewa Yahudawa na buƙatar samun amincewar Larabawa a duk lokacin da za su koma yankin. Haka nan kuma Birtaniya ta yi alƙawarin samar da ƙasar Falasɗinawa cikin shekara 10, idan hakan zai yiwu, inda Falasɗinawa da Yahudawa za su haɗa gwiwa wajen samar da gwamnati, lamarin da zai kai ga ƙarshen ikon da Birtaniya ke yi da yankin, da kuma ƴanta yankin Falasɗinawa.

Duk da cewa hakan ya tamkar nasara ce ga ɓangaren Larabawa, lamarin bai samar da zaman lafiya ba, inda aka riƙa samun rikici tsakanin ƙungiyar ƴan sintiri Yahudawa da dakarun Birtaniya. A shekarun da suka biyo baya sai Turawan Birtaniya suka ga cewa ba za su iya ci gaba da mulkin yankin ba, kuma sun kasa haɗa kan Larabawa da Yahudawa.

Birtaniyar ta kasa rage yawan tuɗaɗar Yahudawa zuwa yankin - kuma wasu na ganin hakan na taɓa ƙimar Birtaniya kasancewar sojojin ruwan Birtaniya sun riƙa amfani da ƙarfi wajen hana jiragen ruwa ɗauke da Yahudawa ƴan gudun hijira shiga yankin na Falasɗinawa.

Yadda sabon yaƙi ya ɓarke tsakanin Isra’ila da Falasɗinawa

7 Oktoba 2023

Yadda kan ƙasashen Afirka ya rabu game da rikicin Isra'ila da Gaza

9 Oktoba 2023

An shigar da Netanyahu tiyata yayin da zanga-zanga ke tsananta a Isra'ila

23 Yuli 2023

Shirin Raba ƙasa:

Taswirar tsarin raba yankin Falasɗinawa tsakanin Falasɗinawa da Isra'ila na MDD

A shekarar 1947, bayan da Birtaniya ta sanar da aniyarta ta ficewa daga yankin Falasɗinu, sai ƙasashen Majalisar Dinkin Duniya suka amince wata matsaya da ake kira 'Resolution 181'. Yarjajeniyar ta yi kira da raba yankin Falasɗinawa zuwa ƙasar Yahudawa da ƙasar Falasɗinawa, yayin da birnin Ƙudus zai zamo ƙarƙashin kulawar Majalisar Ɗinkin Duniya.

Tsarin ya ware kimanin kashi 55% na yankin ga Yahudawa. Kuma hakan ya haɗa har da birane da dama waɗanda Falasɗinawa ne suka fi yawa a cikinsu da kuma yankin gaɓar teku mai matuƙar muhimmanci daga Haifa zuwa Jaffa. Ita kuwa ƙasar Larabawar an ba ta kashi ɗaya ne cikin uku na yankin gaɓar teku ta can ɓangaren kudu. Sai shugabannin ƙabilun Larabawa na yankin a wancan lokaci suka ga cewa yarjejeniyar za ta daƙile musu hanyar amfani da tashoshin jiragen ruwa masu muhimmanci da kuma filayen noma.

Daga nan sai suka yi watsi da tsarin, suka bayyana cewa ba a yi adalci ba, kuma ta ci karo da yarjejeniyar ƴancin kai ta Majalisar Dinkin Duniya. Amma duk da haka Majalisar Dinkin Duniya ta amince da tsarin, tare da samar da ƙasar Yahudawa da ta Larabawa. Watanni kaɗan kafin lokacin da Isra'ila ta shirya ayyana ƴancin kanta, ƙungiyoyin Larabawa ƴan tawaye sun tsohe yankunan matsugunan Yahudawa, yayin da ƙungiyoyin ƴan tawaye na Yahudawa suka ƙaddamar da hari kan ƙauyukan Falasɗinawa, lamarin da ya sanya Falasɗinawan tserewa.

Haka nan kuma bore ga mulkin Turawan Birtaniya ya ƙara ƙamari. A farkon shekarar 1948, Yahudawa ƴan bindiga sun ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare, inda baya ga ƙwato yankunan da aka ware wa Yahudawan, suka kuma ƙwato wasu yankunan da aka ware wa Larabawa.

Yaƙin Larabawa da Isra'ila na farko

A ranar 14 ga watan Mayun 1948 ne mulkin turawan Birtaniya ya zo ƙarshe a yankin, inda kuma nan take Isra'ila ta ayyana ƴancin kanta. Nan take dakarun ƙasashen Syria da Masar da Jordan da Lebanon da Saudiyya da kuma Iraqi suka kai farmaki, inda sojojin Masar da Jordan suka kasance a gaba-gaba. Dakarun Isra'ila sun ci galaba a kan na ƙasashen Larabawa sannan suka ƙwace yankin da aka miƙa wa Larabawa a yarjejeniyar raba yankin ta 1947. Yaƙin ya zo ƙarshe a cikin watan Janairun 1949 lokacin da aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Masar - inda daga baya Lebanon da Jordan da Syria suka shiga cikin yarjejeniyar.

A lokacin da aka cimma yarjejeniyar tsagaita wutan, Isra'ila ta ƙwace iko da kusan ilahirin yankin. Jordan ta mamaye yankin da a ayanzu ake kira Gaɓar Yamma, yayin da Masar ta mamaye Gaza. Sai aka raba Ƙudus zuwa gida biyu, dakarun Isra'ila na iko da yankin yamma yayain da Jordan ke iko da ɓangaren gabas. Sai dai an ci gaba da samun tsahin hankali a yankin cikin shekarun da suka biyo baya kasancewar babu wata ƙwaƙƙwarar yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma.B ayanan hoto,Falasɗinawa lokacin da suke gudu daga garuruwansu a shekarar 1948

"Ƴancin komawa

"Ƴancin komawa" gida ɗaya ne daga cikin manyan buƙatun da Falasɗinawa wanda har yanzu aka kasa warwarewa. Ƙudiri na 194 na Majalisar Dinkin Duniya wanda aka amince da shi a ranar 11 ga watan Disamba, 1948 da sauran ƙasashen duniya duk sun amince da hakkin Falasɗinawa na komawa garuruwansu ko neman diyya. Ƙudirin ya ce "ƴan gudun hijira waɗanda ke da niyyar komawa gidajensu tare da zama cikin lumana da maƙwaftansu na da ƴancin yin hakan, kuma a amince musu cikin hanzari". Sai dai Isra'ila ta ce amin ce wa Falasɗinawa su koma garuruwansu na asali zai iya kawo cikas ga wanzuwarta a matsayin ƙasar Yahudawa, saboda yawan mutanen. Isra'ila ta ce lamari ne da da za a iya magance shi kawai a ƙarƙashin yarjejeniyar da aka samar wadda ta ba ta damar a matsayin ƙasa mai tsaro da zaman lafiya.Yanzu haka Majalisar Dinkin Duniya ta yi rajistar Falasɗinawa kimanin miliyan biyar waɗanda suka zama ƴan gudun hijira (wannan ya ƙunshi ƴan gudun hijira na farko-farko da waɗanda suka biyo bayansu). Kimanin kashi ɗaya cikin uku - sama da Falasɗinawa miliyan 1.5 na rayuwa ne a sansanonin ƴan gudun hijira 58 a Jordan da Lebanon da Syria da Zirin Gaza da Gaɓar Yamma, ciki har da gabashin birnin Ƙudus.

Mabuɗin kome: 'Alamar haske a gaba'

Bayanan hoto,Wani yaro bafalasɗine riƙe da makulli a domin tunawa da gidajen da iyalansa suka rasa Falasɗinawa waɗanda suka gudu a cikin shekarun al-Nakba - sun tafi ne da makullan gidajensu, da nufin cewa za su koma gida ba da daɗewa ba. Sun riƙa bai wa ƴaƴa da jikokinsu irin waɗannan makullai domin tunawa da gidajensu da suka yi asara, kuma a matsayin wata alama ta "ƴancin komawa gida".

Waɗannan makullai na ci gaba da zama wata alama ta sa ran ƴanci da juriya tsakanin Falasɗinawa masu gudun hijira. A 2006 Falasɗinawa sun tuna da shekara 58 bayan faruwar Ibtila'in al-NakbaASALIN HOTON, Bayanan hoto,A 2006 Falasɗinawa sun tuna da shekara 58 bayan faruwar Ibtila'in al-Nakba

Tunawa da ibtila'i (al-Nakba)

A tsawon gwamman shekaru, Falasɗinawa na tunawa da abin da suka kira ibtila'in da ya afka wa ƙasarsu wanda ya tarwatsa su. A shekarar 1998, shugaban hukumar mulkin Falasɗinawa, Yasser Arafat ya ayyana 15 ga watan Mayu a matsayin ranar tunawa da lamarin, a hukumance. A shekarar 2022, a karon farko cikin tarihin Majalisar Dinkin Duniya, Babban zauren majalisar ya buƙaci a tuna da lamarin a ranar 15 ga watan Mayu, 2023. Al-Nakba na ci gaba da tasiri a rayuwar Falasɗinawa. Mutane da dama na cewa ibtila'in da ya afka wa Falasɗinawa a baya na ci gaba da rikiɗewa ta yadda har yanzu babu wata alamar samun masalaha a nan kusa.

Post a Comment

Previous Post Next Post