Da Dumi-Dumi: An Kori Ɗaliban Najeriya A Kasar Burtaniya.

Yadda Faduwar Darajar Naira Ta Sa Aka Kori Ɗaliban Najeriya Daga Birtaniya.

An kori wasu ɗalibai ƴan Najeriya daga makaranta tare da ba su umarnin barin Birtaniya saboda gazawa wajen biyan kuɗin makaranta sakamakon faɗuwar darajar kuɗin ƙasar tasu naira. Hakan dai ya faru ne a Jami'ar Teesside, wadda ta dakatar da ɗaliban daga shiga aji saboda rashin biyan kuɗin makaranta a kan lokaci. Wasu daga cikin waɗanda lamarin ya shafa sun shaida wa BBC cewa, matakin Jami'ar ya sanya sun ji kamar su kashe kansu, inda suka zargi jami'ar da ɗaukar mataki na rashin tausayi.

Mai magana da yawun Jami'ar ya ce rashin biyan kuɗin makaranta ya saɓawa dokar izinin zaman ƙasar, lamarin da ya sa suka sanar da hukumar shigi da fici ta ƙasar halin da ɗaliban suke ciki. Najeriya dai na fama da matsin tattalin arziƙi da faɗuwar darajar kuɗin ƙasar naira, lamarin da ya jefa da yawan ɗaliban ƙasar da ke karatu a Birtaniya cikin halin ha'ula'i. Tashin farashin kayayyaki ya ƙaru da kashi 30 cikin ɗari a Najeriya, lamarin ya ƙara taɓarɓarewa ne a lokacin da tsohuwar gwamnati ta yi ƙoƙarin sauya ƙudin ƙasar da sabbi..

Tunda farko dai, ɗaliban sun gabatar da shaidar da ke nuna suna da isassun kuɗin da za su iya biyan kuɗin makaranta da sauran buƙatu na yau da kullum. Sai dai faɗuwar darajar kuɗin ƙasarsu Najeriya ya sanya yawan kuɗin da suke da su ya ragu, da kuma matakin da hukumar makarantar ta ɗauka na mayar da tsarin biyan kuɗin makarantar kashi bakwai a maimakon sau uku da ake biya a baya..Wasu daga cikin ɗaliban da lamarin ya shafa su 60 da suka bayyana wa BBC sunansu, sun ce sun soma matsa wa Jami'ar lamba domin tallafa masu bayan da aka soma dakatar da wasu ɗaliban daga ɗaukar darasi.

Wasu daga cikinsu sun ce sun tuntuɓi hukumomin da ke bayar da bashi. Adenike Ibrahim Bayanan hoto,Adenike Ibrahim ta kusa kammala karatunta a lokacin da aka soke bizarta. Adenike Ibrahim ta kusa kammala karatunta na shekara biyu, a lokacin da ta kasa biyan kuɗin makaranta na zango guda, lamarin da ya sanya Jami'ar ta kore ta tare da kai sunanta ga hukumar shigi da fici ta Birtaniya. Daga bisani ta samu damar biyan kuɗin da makarantar ke bin ta bashi, sai dai duk da hakan ba a ba ta izinin kammala karatunta ba, an kuma ba ta umarnin barin ƙasar ita da ɗanta.

"Na biya kusan kashi 90 na kudin makarantata, kuma na halarci dukkan darussa," in ji Adenike. "Ba su damu da abin da zai faru da ɗalibansu ba, saboda na yi ƙoƙarin nemansu domin mu cimma yarjejeniya amma lamarin ya ci tura." Adenike Ibrahim ta ce lamarin ya jefa ta cikin "tashin hankali" saboda ba ta san makomar karatunta ba.

"Hankalin yarona ya tashi tun bayan da na shaida masa halin da nake ciki," in ji Adenike Ibrahim.

Babu mafita

Ofishin hukumar shigi da fici ta Birtaniya ya shaida wa ɗaliban da lamarin ya shafa da suka haɗa da Adenike cewa an soke bizarsu saboda sun daina karatu a jami'ar.


Eagle ta ga takardar da aka aika wa ɗaliban, wadda ta ce dole ne ɗaliban su bar ƙasar, kuma "ba su da damar ɗaukar wani mataki kan hakan."


Jami'ar ta ce ta yi "kokari" don tallafa wa ɗaliban da abin ya shafa.

Esther Obigwe ta ce ta yi ƙoƙarin yin magana da Jami'ar kan faɗi-tashin da take wajen biyan kudin makaranta, sai dai ba ta samu wanda zai ba ta amsa daga jami'ar ba sai kawai ta ga an dakatar da ita daga daukar darasi tare da ba ta umarnin barin kasar. " Na halarci dukkan darussa da taron bita, Ina cikin ɗaliban da suka fi kowa mayar da hankali," in ji Esther. "Hakan rashin imani ne. Ina cikin tashin hankali da damuwa ga shi babu wanda zan fadawa." Esther ta ce yawancin ɗaliban sun "kashe kuɗi masu yawa kafin su zo nan."

Jude Salubi

Bayanan hoto,Jude Salubri na fatan Jami'ar za ta sake duba matakin da ta dauka kan ɗaliban. Jude Salubi, wanda ya ce yana karatu ne domin hidimtawa al'umma, ya ce ya yi rabin karatunsa lokacin da aka hana shi shiga makarantar tare da ba shi umarnin barin ƙasar. Bayan haka , yana tafiyar sa'o'i 18 daga Teesside zuwa Liverpool domin yin aiki da zai bashi damar tara kudin da zai biya kuɗin da makarantar da ake bin sa.

"Na biya fam dubu £14,000, ana bina bashin fam dubu £14,000, "In ji Jude. Eagle ta fahimci cewa, wasu daliban da abin ya shafa sun yi nasarar biyan wasu maƙudan kuɗaɗe, amma jami'ar a halin yanzu ta kasa tsoma baki a kan batun bizarsu. Kakakin jami'ar ya ce: "Jami'ar Teesside tana alfahari da kasancewarta wata cibiya ta duniya da ke da yawan ɗalibai amma kuma tana sane da wajibcinta game da bayar da biza da bin ka'ida.

Post a Comment

أحدث أقدم