Yanzu-Yanzu: Barcelona Zata Kori Xavi Saboda Wasu Dalilai .

Da Dumi-Dumi: Barcelona Daya Daga Cikin shahararrun ƙungiyar wasan kwallon Kafa Na Tunanin korar Xavi.

Kungiyar Barcelona na duba yiwuwar korar kocin tawagarta Xavi. A cikin watan Junairu ne, dan shekaru 44 din ya bayyana cewa zai sauka daga mukaminsa a karshen kakar wasa ta bana, amma sai shugaban kungiyar Joan Laporta ya lallashe shi, sai ya sauya shawara. Amma kuma saboda kalamansa a tarukan manema labarai, a yanzu mahukunta kulob din suna fushi da shi kuma suna ganin ya kamata a raba gari da shi.

Kocin tawagar karamar kungiyar Barcelona, Rafael Marquez ne ake tunanin zai maye gurbinsa. A ranar Alhamis bayan sun doke Almeria, Xavi ya ce akwai matukar wuya su iya gogayya da Real Madrid ta fannin kudi. "Ina tunanin ya kamata magoya bayan Barcelona su fahimta a kan yanayi mai sarkakiya da ake ciki, ba za su iya goga kafada da Real Madrid a Sifaniya ba da kuma sauran a nahiyar Turai," in ji Xavi.

Real ta lashe gasar La Liga kuma a yanzu tana jiran buga wasan karshe a gasar zakarun Turai sannan kuma za su dauko Kylian Mbappe daga Paris St-Germain. Xavi ya koma Barca ne daga kungiyar Al Sadd a watan Nuwamban 2021, sannan ya jagoranci kungiyar ta lashe gasar La Liga a shekarar 2023

Post a Comment

أحدث أقدم