Yanzu-Yanzu: Sojoji Sun Kashe 'Yan Bindiga Sama Da 624; Da Nasarar kama 1,051

Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 624, Sun Kama 1,051 A Watan Mayu – DHQ

Dakarun rundunar sojin Nijeriya sun kashe ‘yan ta’adda 624, sun kuma kama 1,051 ciki har da masu kai musu rahoto, sannan sun ceto mutane 563 a watan Mayu, 2024. Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne, ya bayyana hakan ga ‘yan jarida a Abuja.

‘Yancin Kananan Hukumomi: Kotun Koli Ta Bai Wa Jihohi 36 Kwana 7 Su Kare Kansu Ina Kokarin Cika Alkawuran Da Na Dauka – Tinubu. Ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su kasance masu goyon bayan sojoji wajen yaki da ta’addanci da ‘yan fashi da sauran laifuka daban-daban.

Buba ya sake nanata cewa al’ummar kasar nan na da irin rawar da za su taka wajen kawo karshen hare-haren ta’addancin a fadin kasar nan. Kakakin tsaron ya kuma bayyana cewar dakarun sun kwato makamai guda 707.

Labarai Masu Nasaba

Ina Kokarin Cika Alkawuran Da Na Dauka – Tinubu 

Sojojin Nijar Sun Cafke Kasurgumin Dan Bindigar Da Ya Addabi Zamfara Ya ce sun kuma gano bindigogi kirar AK-47 guda 411 da kananan bindigogi guda 234 da sauran muggan makamai. Ragowar kayayyakin da aka kawo ma sata sun hada da litar mai 4,871,470 da danyen mai lita 931,416, in ji Manjo Janar Buba.

Post a Comment

أحدث أقدم