Da Dumi-Dumi: Jerin 'Yan Wasan Real Madrid. Da Suka Ɗauki 6 Champions League.

Nacho Da Modric da Kroos Da Carvajal kowa Ya Ɗauki Champions League 6(Shida)

Nacho da Modric da Kroos da kuma Carvajal, kowanne ya lashe Champions League na shida a tarihi. Ƴan wasan sun bi sawun gwarzon Real Madrid da ya fara ɗaukar babban kofin zakarun Turai shida daga 1956 da 1957 da 1958 da 1959 da 1960 da kuma 1966.Ranar Asabar a Wembley Real Madrid ta lashe La Liga na 15 jimilla da ake kira La Decimoquinta a Landan, inda ƴan wasan hudu kowanne ya ɗauki na shida kamar yadda Paco Gento ke da wannan ƙwazon.

Kenan ƴan wasa biyar ne a tarihi da kowanne ya ɗauki Champions League shida, kuma dukkansu daga Real Madrid, koda yake Kroos ya lashe daya a Bayern Munich. Modric da Nacho da Carvajal duk sun lashe Champions League shida-shida a Real Madrid, yayin da Kroos ya dauki biyar a kungiyar da ɗaya a Bayern Munchen a Wembley a 2013.

A kakar 2013/14 Nacho da Modric da kuma Carvajal suka fara ɗaga babban kofin zakarun Turai a karon farko a Lisbon a Real Madrid. Lokacin da Kroos ya koma Real Madrid ƴan wasa hudun suka lashe na bibiyu a Milan a 2016 da kuma ɗaukar na uku-uku a 2017 a Cardiff .

Haka kuma sun lashe Champions League na hurhudu a 2018 a Kyiv da kuma cin na biyar-biyar 2021/22 a birnin Paris. Shi kuwa Gento shi ne na farko da ya lashe Champions League shida a tarihi a duniya a Real Madrid, kuma tun kan a sauya fasalin sunan kofin

Gento gwarzon ɗan wasan Real Madrid yana cikin ƴan wasan da suka ɗauki biyar a jere a ƙungiyar daga 1956 to 1960. Ya samu damar lashe na shida a 1966, yanzu kaka 58 tsakani, an samu waɗanda suka yi kan-kan-kan da shi a yawan lashe kofin kuma a Real Madrid.

Post a Comment

Previous Post Next Post