Yanzu-Yanzu: Bayan Shekaru 13, Tsofaffin Ma'aikatan Zamfara Sun Samu ₦5B

Yanzu-Yanzu: Bayan Shekaru 13, Tsofaffin Ma'aikatan Zamfara Sun Samu  ₦5B

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya biya sama da Naira biliyan 5 ga ma’aikatan gwamnatin da suka yi ritaya bayan shafe shekaru 13 ba tare da an biya su kuɗin sallama ba. An fara biyan ne tun a watan Fabrairu bayan gudanar da tsarin tantance waɗanda suka yi ritayar.

 A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, jihar ta biya Naira biliyan biyar da miliyan ɗari uku da arba’in da bakwai da Naira dubu ɗari biyu da arba’in da uku da Naira ɗari biyu da goma (5,347,243,210.00) ga waɗanda suka yi ritaya daga jihar da kuma ƙananan hukumomi a rukunnai biyar.

Shekara Ɗaya A Mulki: Gwamna Lawal Ya Ƙaddamar Da Manyan Ayyuka A Ƙananan Hukumomin Zamfara. Shekara Ɗaya A Mulki: Ayyukan Ci Gaban Da Muke Yi Na Samun Tagomashi A Zamfara – Gwamna Lawal Sanarwar ta bayyana cewa an biya kuɗin sallama daga aiki ga malaman ƙananan hukumomi da na firamare 2,209 da ma’aikatan jihar 1,642 da suka yi ritaya. Musamman ma’aikatan jihar su 4,198 da suka yi ritaya, jimmilar ₦8,095,948,906.63.

A cikin wannan rukunin na farko ƴan fansho 1,382 da aka tabbatar sun karɓi ₦2,336,271,961.37, yayin da kashi na biyar aka biya masu karɓar fansho 260 ₦510,094,956.35. Kazalika, malaman ƙananan hukumomi da na firamare 465 da suka yi ritaya sun sami ₦500,969,762.47 a kashi na biyar.

A dunkule, an biya malaman ƙananan hukumomi da na firamare 2,209 da suka yi ritaya Naira ₦2,500,876,293.16 a rukuni biyar, wanda hakan ya haɗar da waɗanda suka yi ritaya a tsakanin shekarar 2012 zuwa 2019.

Post a Comment

Previous Post Next Post