Hedkwatar Tsaron Amurka Ta Shaida Wa 'Ƴan Majalisar Dokokin Ƙasar Ranar Alhamis Cewa A HukumanceBa Su Bai Wa Dakarun Amurka Umarnin Barin Ƙasar Ba

 Hedkwatar Tsaron Amurka Ta Shaida Wa 'Ƴan Majalisar Dokokin Ƙasar Ranar Alhamis Cewa A Hukumance Sojojin Nijar Ba Su Bai Wa Dakarun Amurka Umarnin Barin Ƙasar Ba, Tana Mai Cewa Ta Samu Bayanai Masu Harshen-Damo Kan Matakin Korar Dakarun Nasu Daga Nijar.



Celeste Wallander, mataimakiyar sakataren tsaron Amurka kan ƙasashen duniya, ta shaida wa Kwamitin Harkokin Sojoji na Majalisar Wakilan ƙasar cewa a hukumance kawo yanzu gwamnatin sojojin Nijar, wadda aka fi sani da CNSP, ba ta umarci sojojin Amurka su fita daga ƙasar ba.

Wallander ta ce gwamnatin sojin Nijar ta soke yarjejeniyar da ta bai wa dakarun Amurka damar zama a ƙasar. Amma ta ce sojojin sun "tabbatar mana cewa za a kare lafiyar dakarun Amurka kuma ba za su ɗauki wani mataki da zai cutar da su ba.”

Amurka tana da dakaru kusan 650 tare da ɗaruruwan masu taimaka musu a Nijar, inda suke yaƙi da ta'addanci. Sai dai a watan Yulin da ya gabata sojoji sun kifar da gwamnatin dimokuraɗiyya sannan daga bisani suka kori dakarun Faransa daga ƙasar.

Wallander ta ce Amurka tana yin nazari kan wasu hanyoyi na ci gaba da yaƙi da ta'addanci a yankin.

Yawancin dakarun Amurka da ke Njar suna zaune ne a sansani guda ɗaya kuma suna ci gaba da gudanar da aiki da jirage marasa matuƙa, ko da yake suna yin hakan ne da zummar bai wa kansu kariya, a cewar mataimakiyar kakakin hedkwatar tsaron Amurka Sabrina Singh.

“Ana ci gaba da tattaunawa da gwamnatin soji ta CNSP domin samun mafita,” in ji Singh.

Comments

Popular posts from this blog

Yanzu-Yanzu: Babbar kotun koli Ta Kasa Nigeria Ta Umarci Jam'iyyar PDP Ta Bai wa Tsohon Gwamnan Jigawa Daman Fitowa Takarar Shugabanci Jam'iyyar.

Abun-Mamaki: Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Usman Bauchi /Sababbin kabarai na hausa EagleNewsHausa

Ana Wata Ga Wata: 'Yan Bindiga Sunyi Garkuwa Da Mata 12.