Da Dumi-Dumi: "Mun Musa Cimma Matsayia Akan Sabon Tsarin Mafi Karancin Albashin Ma'aikata" Gwamna Uzodimmo

"Mun kusa Cimma Matsayia Akan Sabon Tsarin Albashin Ma'aikata". Gwamna uzodimmo.

Gwamnan jihar Imo State, Hope Uzodimma, ya ce kwamitin tsara mafi ƙarancin albashin ma'aikatan Najeriya ya kusa cimma matsaya a kan sabon albashin. A ƙarshen taron kwamitin, gwamna Uzodimma, ya ce bayan shafe sa'oi 12 ana tattaunawa tsakanin mabobin kwamitin, an cimma matsaya kan shawarar da ta dace su bai wa gwamnati.

Gidan talabijin É—in Channels ya ruwaito gwamna Uzodimma, ya na cewa: “Mun yi tattauwa mai daÉ—in gaske kuma ana iya cewa mun cimma matsaya a matakinmu na Æ™aramin kwamitim, don haka idan muka je ga babban kwamiti komai zai tafi lafiya.” Ya yi bayanin cewa kwamitin ya tuntuÉ“i duk waÉ—anda ya kamata, kuma sakamakon rahoton zai zamo abin da ake sa ran yin amfani da shi wajen cimma matsaya a babban kwamitin da zai yi aiki na gaba a kan sabon albashin.


Gamayyar kungiyoyin ƙwadago a Najeriya dai ta ƙi amincewa da tayin naira 60,0000 da gwamnati ta yi mata a matsayin mafi ƙarancin albashi, lamarin da ya sa ta fara yajin aikin gama gari daga ranar Litinin. Sai dai gamayayar ta dakatar da yajin aikin a ranar Talata bayan gwamnatin tarayya ta yi alƙawarin ƙara wa a kan tayin ta na farko, kuma hakan ya buɗe sabuwar hanyar tattaunawa a kan batun.

Post a Comment

Previous Post Next Post