Hajjin 2024: Abubuwan Da Suka Kamata A Sani

Hajjin 2024: Abubuwan Da Suka Kamata A Sani

Hukumar kididdiga ta kasar Saudiyya GASTAT ta fitar da cikakkun alkaluman da suka shafi aikin hajjin shekarar 2024, inda ta bayyana cewa alhazai 1,833,164 ne suka gudanar da aikin hajjin bana a Makka. Wanda hakan ya nuna yadda Alhazai dabam-dabam daga sassan duniya suka halarci aikin Hajjin Bana.

A bangaren jinsi a tsakanin Alhazan wannan shekarar, an samu maza 958,137 da mata 875,027 a gaba ki dayan Alhaza da suka gabatar da ibadar. Mafiya yawa daga cikin mahajjatan da adadin da sun ya kai 1,611,310, sun fito ne daga kasashen ketare, yayin da 221,854 suka kasance mahajjatan cikin gida ‘yan kasar Saudiyya.

Kamfanin Kera Motoci Masu Amfani Da Lantarki Na Sin Ya Shiga Kasuwar Kenya, Mutane 75,000 Sun Kamu Da HIV, 45,000 Sun Rasu A Shekarar 2023 – NACA DG. Kason Nahiyoyin Da Suka Halarci Kasar Saudiyya

Kididdigar alkalumman yawan mahajjatan bana ta nuna kashi 63.3% na mahajjatan Asiyawa ne (wadanda suka fito daga yankin Asiya) wadanda ba Larabawa ba, wanda ya sa wannan ya zama rukuni mafi yawa a mahajjatan bana. Alhazan da suka kasance larabawa kuwa sun kunshi kashi 22.3%, sai kuma ‘yan Nahiyar Afirka wadanda ba larabawa da suka kunshi kashi 11.3%.

Sauran kashin kuma wadanda suka fito daga nahiyar Turai da Austrilia sun kunshi kashi 3.2% daga cikin yawan mahajjatan banan.

Labarai Masu Nasaba

Wani Alhaji Ya Sake Mayar Da Makudan Kudaden Da Ya Tsinta A Makkah

Rahoto Ya Bankado ‘Yan Siyasa Da Jami’an Tsaron Nijeriya 200 Masu Kadarori A Dubai

 Hanyoyin Sufurin Da Akayi Amfani Da Su

Dangane da hanyoyin sufurin da aka yi amfani da su kuwa, mafi yawan alhazai wanda addadinsu ya kai 1,546,345, sun isa kasar ne ta jirgin sama. Sai kuma mahajjata kimanin 60,251 da suka shiga kasar Saudiyya ta Motaci da kuma jiragen kasa. Sai Kuma mahajjata 4,714 da suka isa kasar ta ruwa.

Rayukan Da Aka Rasa Sai dai kash, a lokacin aikin Hajjin na bana, an yi asarar rayuka da dama. Ministan lafiya na Saudiyya ya tabbatar da cewa mahajjata 1,301 ne suka rasu a yayin gudanar da aikin hajjin. Musamman ma, kashi 83% na wannan mace-macen sun shafi mutanen da ba su da ingantacciyar takardar izinin gudanar da aikin Hajjin ne.


Alkaluma da abubuwan da suka faru na Hajjin 2024 sun nuna yadda ibadar aikin hajjin ke tara mutane daga sassa daban-dabam na duniya da kuma irin yadda al’ummar muslulmi a duniya suka dauki ibadar da ta kasance cikin rukunai ko ginshikai na addinin musulunci.

Duk da irin kalubalen da ake fuskanta, miliyoyin musulmi sun yi nasarar kammala wannan aikin na ibada, lamarin da ke nuni da jajircewa da sadaukarwar mahajjata da kuma irin kokarin da mahukuntan Saudiyya suke yi

Post a Comment

Previous Post Next Post