Yanzu-Yanzu: 'Ƴan Bindiga Sun Sace Mahaifiyar Shahararan Mawaƙin Nan Dauda Kahutu Rarara

'Ƴan Bindiga' Sun Sace Mahaifiyar Mawaƙi Dauda Kahutu Rarara 


Hukumomi a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya sun tabbatar da sace mahaifiyar sanannen mawaƙin Hausa, Dauda Kahutu Rarara.

A tattaunawarsa da BBC, kwamishinan tsaro na jihar, Nasiru Mu'azu ya ce an sace dattijuwar ce a daren Juma'a a ƙauyen Kahutu da ke ƙaramar hukumar Ɗanja.

Mu'azu ya ce wadanda suka sace matar sun yi hakan ta hanyar bi ta bayan gida, inda suka sace ta ba tare da jami'an da ke tsaron gidan sun sani ba.

Ya kuma bayyana cewa tuni aka tura jami'an tsaro waɗanda suka bazama cikin dazuka domin bin sawun ƴan bindigan

Katsina na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fuskantar matsalar tsaro, inda ƴan bindiga ke kashewa tare da yin garkuwa da mutane. Hakan ya durƙusar da sana'o'i da harkoki na yau da kullum.

Post a Comment

Previous Post Next Post