Inalillahi! An kashe Mutane Sama Da 120 A Kauyen Sudan, Lamarin Ya Tada Hankalin Duniya

Kisan Mutum 150 A wani Ƙauyen Sudan Ya Tayar Da Hankalin Duniya.

Aƙalla mutum 150 ne ake tunanin an kashe a kisan kiyashin da aka yi a wani ƙauye da ke tsakiyar ƙasar Sudan, wanda ake zargin mayaƙan ƴan tawaye na RSF da aikatawa. Yanzu sama da shekara ɗaya ke nan mayaƙan ƙungiyar RSF na yaƙi da dakarun gwamnati a wani yunƙuri na ƙwace iko da ƙasar.

Har yanzu RSF ba ta ce uffan ba game da zargin da ake yi mata na kisan mazauna ƙauyen, sai dai a jiya Alhamis ƙungiyar ta bugi ƙirjin cewa ta kai hare-hare kan wasu cibiyoyin dakarun sojin gwamnati guda biyu..Bidiyon da ya riƙa yawo a shafukan sada zumunta bayan harin na ranar Laraba ya nuna yadda aka shirya gawawwaki bila-adadin waɗanda za a yi wa jana'iza a garin Wad al-Nourah da ke jihar Gezira.

Wani mai fafatuka - ɗan wata ƙungiya mai rajin ganin ƙasar ta koma kan tafarkin mulkin dimokuradiyya ne ya naɗi bidiyon. Ƙungiyar masu fafutikar ta Madani Resistance Committe ta ce a yanzu "tana jiran samun jimillar mutanen da aka kashe da kuma wadanda aka raunata" a harin. Har yanzu ba a san dalilin aikata wannan kashe-kashe ba - sai dai ana zargin cewa sau biyu mayaƙan RSF suna ƙaddamar da hari kan ƙauyen a ranar Laraba.

Hafiz Mohamad, wanda jami'i ne a ƙungiyar kare hakkin bil'adama ta Justice Africa Sudan ya shaida wa BBC cewa har yanzu akwai mutanen da ba a san inda suke ba sannan yana "da wahala a iya ƙididdige mutane da aka kashe domin har yanzu akwai mayaƙan RSF da ke yankin suna satar kayan al'umma". Gwamnatin Sudan ta yi kira ga ƙasashen duniya su yi alla-wadai da kashe-kashen na Wad al-Nourah.

A watan Disamba ne dakarun RSF suka ƙwace iko da jihar ta Gezira wadda ke kudu da Khartoum, babban birnin Sudan, kuma ana zargin su da aikata laifuka kan fararen hula, duk da cewa sun musanta hakan. Duk da haka ana ci gaba da gwabza faɗa tsakanin dakarun gwamnati da na RSF a birnin El Fasher, wanda ke a yankin Darfur da ke yammacin ƙasar.An yi ƙiyasin cewa mutum 15,000 ne aka kashe a faɗin Sudan tun bayan da yaƙi ya ɓarke a ƙasar cikin watan Afrilun 2023

Post a Comment

أحدث أقدم