Turƙashi: Ƙungiyar ƙwadago Zata Dau Mataki Idan Har Dai Ba Ta Samu Biyan Buƙata Ba.


Wane Matakin Ƙungiyar ƙwadago Za Ta Ɗauka Idan Ba Ta Samu Biyan Buƙata Ba?

A ranar Litinin ɗin nan ne ake sa ran kammala tattaunawa kan mafi ƙarancin albashin ma’aikata da ake yi tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyar ƙwadago, yayin da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadagon Najeriya NLC da TUC ke jiran matakin da shugaban kasa Bola Tinubu ya ɗauka kan batun biyan mafi ƙarancin albashi na N250,000.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne kwamitin da ke kula da mafi ƙarancin albashi na ƙasa ya kammala taronsa, inda gwamnatin tarayya da ƙungiyoyi masu zaman kansu suka cimma matsaya kan kuɗirin naira 62,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin ma'aikata. A halin da ake ciki dai a yanzu, ƙungiyayin ƙwadagon biyu sun dage a kan biyan mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata na naira 250,000.

Sai dai kungiyar gwamnonin Najeriya ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cewa duk wani mafi ƙarancin albashi da ya haura N60,000 ba zai ɗore ba.

Illar da yajin aiki ke yi wa ƙasa4 Yuni 2024

Yadda ƴan ƙwadago suka tsayar da ayyuka cak a Najeriya 3 Yuni 2024

Mene ne abin yi na gaba?

An tuntunɓi ɗaya daga cikin shugabannin ƙungiyar ta ƙwadago dangane da matsayin da za su ɗauka na gaba idan dai har ba su cimma wata matsaya ba da gwamnati. "Yanzu dai muna cikin taro inda muke tattaunawa...idan mun gama zan yi muku bayani." In ji jami'in ƙungiyar ƙwadagon.

Ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya dai sun jingine yajin aikin ne da suka fara a ranar Litinin, bayan cimma yarjejeniya da gwamnatin tarayyar ƙasar a yammacin ranar, inda kuma suka bayar da wa'adin mako guda. Tun farko manyan ƙungiyoyin biyu sun kira yajin aikin ne bayan gaza cimma matsaya a kan albashin ma'aikata mafi ƙanƙanta a ƙasar.

An kwashe tsawon lokaci ana kai ruwa rana tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin ƙwadago na 'Nigeria Labour Congress da Trade Union Congress' a ƙasar ta Najeriya game da batun ƙarin albashin. Sai dai abin ya ci tura bayan da ƙungiyoyin ƙwadagon suka zargi gwamnati da rashin mayar da hankali kan tattaunawar.

Post a Comment

أحدث أقدم