Wata Sabuwa: Hukumar NDLEA Ta Kama Wasu Maniyyta Da Hodar Iblis

Hukumar NDLEA Ta kama Maniyyata Da Hodar Ibilis A Legas


Jami’an hukumar yaƙi da masu ta'ammali da miyagun ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA, sun kama wasu maniyyata da ke shirin zuwa aikin hajji da hodar ibilis a wani sumame da suka kai a otal din Emerald da ke Ladipo a jihar Legas, jiya Laraba.

Daraktan yaɗa labarai na hukumar, Femi Babafemi ne ya tabbatar da kamen. Waɗanda aka kama sun haɗa da wani Usman Kamorudeen da Olasunkanmi Owolabi da Fatai Yekini, da kuma wata mata, Ayinla Kemi.

Jami’an hukumar ta NDLEA sun gano kwalayen hodar iblis 200 kowannensu nauyinsa ya kai kilogiram 2.20, waɗanda ake zargin za su haɗiye kafin su tashi zuwa ƙasa mai tsarki. Shugaban hukumar, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya) ya yaba wa jami'an hukumar bisa nasarar da suka samu ta cafke mutanen.

Ya kuma jaddada cewa hukumar za ta ci gaba da bin diddigi tare da kamo mutanen da ke yunƙurin amfani da addini wajen aikata miyagun laifuka. Marwa ya bayyana muhimmancin kare martabar ƙasar daga irin waɗannan munanan ayyuka. Sannan ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa hukumar NDLEA za ta haɗa kai da takwarorinsu na Saudiyya domin ganowa tare da damƙe masu ayyukan safarar miyagun ƙwayoyi.

Post a Comment

أحدث أقدم