Wata Sabuwa: Matsanancin Zafi Yayi Sanadayar Mutuwar Mutane Da Dama A Pakistan

Tsananin Zafi Na Ci Gaba Da Kashe Mutane A Pakistan

Jami'an kiwon lafiya a Pakistan sun ba da rahoton ƙaruwar mace-mace sakamakon tsananin zafi inda lardin Sindh ne ya fi fuskantar bala'in zafin da har yanayin zafi ya tashi zuwa digiri arba'in da bakwai a ma'aunin salshiyos.

A Karachi kuma, birni mafi girma, sama da mutum 260 ne aka kwantar a wani babban asibiti da zazzabin cizon sauro tun ranar Lahadi.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta gida ta bayar da rahoton tattara fiye da sau uku adadin gawarwakin mutanen da suka mutu sakamakon tsananin zafi a cikin ‘yan kwanakin nan. Domin a sassauta lamarin ne aka kafa cibiyoyin ba da agajin gaggawa ga jama'a.

A halin da ake ciki, mazauna birnin Karachi sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da katsewar wutar lantarki da ya kawo cikas ga samun iskar fankoki da na AC da kuma tsadar wutar Lantarki.

Post a Comment

Previous Post Next Post