Wata Sabuwa: An Halasata Yi Amfani Da Tabar Wiwi A Brazi

 An Halasata Amfani Da Tabar wiwi wadda Ba Ta Wuce Ƙima Ba A Brazil

Kotun ƙoli a Brazil ta kaɗa ƙuri'ar amincewa da mallakar tabar wiwi, don amfanin kai. Daga yanzu wadanda aka kama da kunshin ganyen tabar ɗan kaɗan ba za su fuskanci hukuncin aikata laifi ba, amma ana yi cin su tara idan ta zarta kima.

Yau Laraba ne dai kotu za ta ci gaba da zama domin yanke hukunci a kan yawan miyagun ƙwayoyi da za a ƙayyade.

Alkalan kotun sun ce dole ne ya kasance akwai bambanci wajen hukunta masu amfani da kayan maye da kuma masu dillancinsu.

Masu fafutuka sun ce hukuncin zai amfanar da dubban jama'a, musamman matalauta da marasa galihu a cikin al'umma, wadanda ake tuhuma da daure su a gidan yari idan aka kama su da tabar wiwi.

Post a Comment

Previous Post Next Post