Yanzu-Yanzu: Sojojin Isra'il Sun Yi Nasarar Ceto Mutum 4 Daga Cikin Waɗanda A Kayi Garkuwa Da Su.

 

Sojin Isra'ila Sun Ce Sun Ceto Mutum 4 Cikin Waɗanda Da Hamas Ta Yi Garkuwa Da Su.

Dakarun Isra'ila sun ce sun ceto ceto mutum huɗu daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su, yayin wani samame da suka kai Nuseirat a tsakiyar Gaza. Mutanen sun hada da Noa Argamani da Almog Meir Jan da Andrey Kozlov da kuma Shlomi Ziv.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce mutanen suna cikin waɗanda Hamas ta yi garkuwa da su a harin da ta kai ranar 7 ga watan Oktoban bara, kuma ta tabbatar da cewa suna cikin ƙoshin lafiya.

 Rahotanni sun ce Firaiminista Benjamin Netanyahu ya zanta ta waya da ɗaya daga cikin mutanen da aka ceto mai suna Noa Argamani. Akwai kuma rahotannin da ke cewa an kashe mutane aƙalla 50, ciki harda da ƙananan yara a lokacin samamen.

Post a Comment

أحدث أقدم