Yanzu-Yanzu: A Yau Ne Ake Gudanar Da shari'a Masarautar Kano.

Yau Ake Gudanar Da Shari'a Kan Masarautar Kano

A yau Alhamis ne babbar kotun tarayya da ke Kano za ta fara zaman sauraron ƙarar da Aminu Babba Ɗan'agundi ya shigar gabanta inda yake ƙalubalantar matakin majalisar dokokin jihar ta Kano na rushe masarautu biyar, tare da cire Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin kano, da mayar da Muhammadu Sanusi II, a kan sarautar.

Dambarwar sarautar ta kai ga Muhammadu Sanusi na biyu, wanda gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf ya mayar a kan karaga yake zama a gidan sarkin, tare da zama a fadar da ke ƙofar kudu, yayin da shi ma Aminu Ado Bayero ke zama a gidan sarki da ke unguwar Nassarawa.

Al'ummar Najeriya da dama musamman na jihar ta Kano sun zuba ido don ganin yadda za ta kaya ganin yadda mutanen biyu ke ja-ni-in-ja-ka kan masarautar Kanon mai ɗinbim tarihi. An jibge jami'an tsaro a hanyoyin zuwa babbar kotun, inda ake sa ran Mai Shari'a Abdullah Muhammad Liman zai fara sauraron ɓangarorin da ke cikin wannan ƙara.

Post a Comment

أحدث أقدم