Da Dumi-Dumi: 'Ƴan Ta’adda 284 Sun Miƙa Wuya Ga Sojojin Haɗaka

Ƴan Ta’adda 284 Sun Miƙa Wuya Ga Sojojin Haɗaka.

Nasarar yaki da ta’addanci na ci gagaba da samuwa, domin a tsakanin 10 zuwa 17 ga Yuli, 2024, mayakan Boko Haram 284 tare da iyalansu sun mika wuya ga rundunar hadin Gwuiwa ta kasa da kasa (MNJTF) a Kamaru.

 Laftanar Kanal Abubakar Abdullahi, Shugaban sashen Hulda da Jama’a, ya bayyana cewa dakarun sashi na 1 sun karbi mayaka biyar a Wulgo a ranar 11 ga Yuli, 2024. Bayanai na farko sun nuna cewa wadannan mayakan sun fito ne daga Tumbuma da Kutumgulla a karamar kukumar Marte ta Jihar Borno, Nijeriya.

A wannan ranar, Malum Kori Bukar, mai shekaru 50 da ya tsere daga maboyar Jibilaram, ya mika wuya ga dakarun. Haka zalika, mayaka 19 sun mika wuya a Madaya, Arewa Maso Gabashin Kamaru, da wasu 11 a Wulgo. 

A ranar 12 ga Yuli, mayaka 64, ciki har da manya shida, mata 20, da yara 38, sun mika wuya a Bonderi, Kamaru.

An Tafka Gumurzu, Sojoji Sun Kashe Ƴan Boko Haram Da Yawa, Wasu Sun Miƙa Wuya

Boko Haram Sun Sace Wani Alkali Da Matarsa Tare Da Awon-Gaba Da Wasu Mutane A Borno

A ranakun da suka biyo baya, 27 mayaka sun mika wuya a ranar 13 ga Yuli, 102 a ranar 15 ga Yuli, da wasu biyar a ranar 16 ga Yuli. A ranar 17 ga Yuli, mayaka 48, ciki har da maza 10 manya, mata 15, da yara 23, sun mika wuya.

Ƴan Ta'adda

Bincike na farko ya nuna cewa wadannan mutane 48 da suka mika wuya a ranar 17 ga Yuli sun fito ne daga al’ummomin Nijeriya. An mika su ga dakarun Operation Hadin Kai domin daukar matakan da suka dace.

Labarai Masu Nasaba

Sojojin Sama Sun Yi Lugudan Wuta Kan Ƴan Ta’adda A Kaduna

Kash: Ɗan Fasa-Ƙwauri Ya Hallaka Jami’in Kwastan A Jigawa.

Ƴan Ta'adda

Mika wuyan da ake cigaba da samu yana nuna kokarin da ake yi na tarwatsa cibiyoyin ‘yan ta’adda a yankin

Post a Comment

أحدث أقدم