Yanzu-Yanzu: Hukumar Ƙarshe Gobara Ta Kano Ta Ceto Mutane 154 Da Kadarorin Naira Mikyan 8.


Hukumar Kashe Gobara Ta Kano Ta Ceto Mutum 154 Da Kadarorin Naira Miliyan 80 A Watan Yuli.

Hukumar kashe gobara

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce ta ceci mutane 154 da kadarori da darajar kuɗinsu ya kai naira miliyan 80 daga aukuwar gobara 13 daban-daban a watan Yuli.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Alhaji Saminu Abdullahi, ne ya bayyana hakan cikin wata hira da ya yi da manema labarai yau Litinin a Kano.


NIS Ta Fara Binciken Wata Mata Da Ta Yayyaga Fasfonta A Filin Jiragen Sama Na Legas

Kungiyar NLC Ta Nemi Rundunar ‘Yan sanda Ta Nemi Afuwarta 

Abdullahi, ya ce duk da wannan namijin ƙoƙari kimanin mutum 150 da dabbobi da dama sun mutu sakamakon gobarar da aka yi a tsawon lokacin, bisa yadda aka yi nazari a kai yayin da kuma gobara ta lalata dukiya da ta kai darajar naira miliyan 27.

Labarai Masu Nasaba

An Yi Asara Kimanin Naira Biliyan 500 Sakamakon Zanga-zanga – Minista

Gwamna Bago Ya Yi Allah-wadai Da Kona Coci A Neja.


Ya shawarci jama’a da su riƙa kula da wuta tare da tabbatar da sun kashe duk wata na’urar lantarki kafin barin wuraren da suke aiki ko harkokinsu na kasuwanci, musamman masu dafa abinci da sayar da abincin dare.

Ya kuma buƙaci masu ababen hawa da su yi taka-tsan-tsan a lokacin damina domin guje wa abubuwan da ka iya aukuwa wanda ba a sani ba.

Post a Comment

أحدث أقدم