Da Ɗumi-Ɗumi: NNPC Ya Ƙara Farashin Man Fetur Zuwa 855 A Kowace Lita.

NNPC Ya Ƙara Farashin Man Fetur Zuwa 855 Kan Kowace Lita.

Wasu gidajen sayar da man fetur na kamfanin mai na ƙasa (NNPC) l, na sayar da man fetur a kan Naira ₦855 ga kowace lita a wasu sassan Legas.

Wannan na cikin wani faifan bidiyo ya nuna a shafukan sada zumunta. Matatar Dangote Ta Fara Shirin Sayar Da Mai A Faɗin Nijeriya

Tinubu Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Hajiya Dada Yar’adua

Bidiyon wanda wani mai saye ya nuna rashin jin daɗinsa ya yaɗa, ya nuna cewa farashin litar kan wane kan famfo a gidan mai da ke Ikoyi, a Legas ya kai Naira 855 kan kowace lita.

Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa game da tsadar man fetur wanda kwanaki shida da suka gabata, inda rahotannin kafafen yada labarai suka nuna cewa farashin man na iya yin tashin gwauron zabi zuwa Naira 1,300 kan kowacce lita, saboda matsalar kuɗi da NNPC ke fuskanta.


Kamfanin wanda shi ne kaɗai mai shigo da man fetur a Nijeriya, ya sha musanta batun biyan tallafi, inda ya ce kawai yana sanya ido ne game da kudin shigo da man kuma tare da shaida ƙalubalen tsadar kayan man.

Labarai Masu Nasaba

Matatar Dangote Ta Fara Shirin Sayar Da Mai A Faɗin Nijeriya

Kwamitin Majalisa Ya Nemi A Rage Wa ‘Yan Majlisa Albashi


Ana wannan cece-kuce ne, matatar man Dangote ta sanar da fara sayar da mai, inda kamfanin NNPC ke shirin zama na farko da zai fara siya wanda hakan zai yi tasiri ga farashin man fetur a kasuwar man ƙasar nan.

A halin da ake ciki, gwamnatin tarayya ta bakin ministan albarkatun man fetur Heineken Lokpobiri, ta musanta rahotannin da ke cewa ma’aikatar man fetur ta umarci NNPC ya sayar da mai sama da farashin da aka amince da shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post