Yanzu-Yanzu: Ecowas Zata Samar Da Rundunar Dakaru 5,000 Don kawo Ƙarshe Ta'addaci

 Ecowas Za Ta Samar Da Runduna Ta Dakaru 5,000 Don Yaki Da Ta'addanci

Ƙungiyar Ecowas ta ce tana shirin kafa runduna ta dakaru 5,000 domin yakar ta'addanci a yankinta na yammacin Afrika. 

Shugaban hukumar Ecowas Omar Touray wanda ya bayyana haka a wani taron tsaro da aka gudanar a Abuja ya ce an kai hare-hare 1,605 tsakanin watan Janairu zuwa Agustan 2024 a yammacin Afirka, kuma an samu hasarar rayuka 6,956.

Ya ce, "bisa umarnin shugabannin ƙasashen Ecowas, akwai yunƙuri da ake na samar da runduna ta dakaru 5,000 domin yaƙi da ta'addanci."

 Mali da Burkina Faso da Niger da Nigeria ne ƙasashen da matsalar tsaro ta fi addaba a yankin.

Mista Touray, ya ce a Burkina Faso an kai hare-hare 611 attacks inda aka kashe mutum 3,810. A Mali na kai hare-hare 546 inda aka kashe mutum 1424. 

A Najeriya kuma an kai hare-hare 238 yayin da kuma aka kashe mutum 905, sai Nijar inda aka kai hare-hare153 tare da samun hasarar rayuka 676. 

An kuma kai hare-hare 44 a Benin da hasarar rayuka 66. Sai Togo inda aka kai hare-hare 13 da hasarar rayuka 75.

Post a Comment

أحدث أقدم