Yanzu-Yanzu: Shugaban Iran Yayi Gargaɗi Ga Isra'ila.

Shugaban Iran Yayi Gargaɗi Ga Isra'ila.

Shugaban Iran Massoud Pezeshkian ya kare matakin harin da ƙasarsa ta kai tare da yin gargaɗi ga Isra'ila.

A shafinsa na X, shugaban ya ce "bisa la'akari da haƙƙin Iran tare da manufar zaman lafiya da tsaron Iran da yankin, an mayar da martani ga Isra'ila don kare muradun Iran da ƴan ƙasa."

Da ambaci Netanyahu, inda ya ce Firaministan Isra'ila ya sani cewa "Iran ba mayyar yaƙi ba ce, amma za ta kare kanta daga duk wata barazana.

Ya yi gargaɗi ga Isra'ila cewa wannan harin kamar kyaftawar ido ne" na ƙarfin Iran da kuma kaucewa shiga yaƙi da Iran..

Wannan na zuwa yayin da rundunar sojin Isra'ila ta ce za ta ƙaddamar da harin martani cikin gaggawa ba tare da ɓata lokaci ba.

Post a Comment

أحدث أقدم