Yanzu-Yanzu: Zanga-Zanga Ta Ɓarke A Ƙasar Ghana

Matasa Sun Sake Fita Zanga-Zanga Domin Neman A Saki Ƴan Uwansu A Ƙasar Ghana.

Ƙungiyoyin matasa a Ghana sun hau kan titunan biranen ƙasar domin yin zanga-zangar neman a saki masu zanga-zanga 50 da wata kotu ta bai wa ƴan sanda damar tsare su a makon da ya gabata.

Wata zanga-zangar kwana uku ta nuna ƙin amince wa da haƙar ma'adanai a ƙasar ba bisa ka'ida ba ta janyo arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami'an tsaro al'amarin da ya janyo akakama masu zanga-zangar da dama bisa tuhumar haɗuwa ba bisa ƙa'ida ba.

Da safiyar Alhamis ne kuma ɗaruruwan masu zanga-zangar suka yi dafifi inda suka hau titunan birnin Accra suna neman a saki mutum 50 ɗin da ake tsare da su.

Mutanen ƙasar da dama dai sun alawadai da abin da ƴansandan da kotu suka yi na tsare matasan har tsawon makonni biyu.

Ƙasar Ghana dai ita ce wadda ta fi kowacce ƙasa albarkatun gwal a nahiyar Afirka, to sai dai ƙasar tana fama da matsalar haƙar ma'adan ba bisa ƙa'ida ba wani al'amari da ya jawo gurɓatar muhalli ciki har da kogu.

Post a Comment

أحدث أقدم