Posts

Showing posts from February, 2024

TIRKASHI: Yadda Google Map Ya Jagoranci 'Yan bautar kasa Zuwa Gidan 'Yan Bindiga A Sokoto - Shehu Sani

Image
  Tsohon dan majalisa kuma mai fafutukar jin dadin jama'a, Sanata Shehu Sani, ya koka kan karuwar satar mutane da fashi da makami a Najeriya. Sani ya bayyana cewa, wani matashi dan bautar kasa, wanda a kwanan baya ya kubuta daga hannun ‘yan bindigar, ya bayyana yadda taswirar Google da suka yi amfani da ita a yayin da suke tafiya jihar Sakkwato ya kai su ga yankin ‘yan bindigar. Tsohon dan majalisar, wanda ya bayyana hakan a shafinsa na X (Twitter) ya rubuta cewa: "Daya daga cikin Matasan da suka tsere daga hannun 'yan bindigar ya bayyana cewa sun yi amfani da google map a hanyarsu ta zuwa Sokoto inda hakan ya kai su ga gidan 'yan bindiga." Haryanzu Arewacin Nageriya musamman Arewa maso Yamma na fama da matsalar tsaro wanda ya ha'da hare haren 'yan bindiga da 'yan gashi da makami.

TAURARI BIYU DAGA GIDA ƊAYA

Image
Hajara Ibrahim Ɗan'azumi ita ce gwarzuwar shekara a gasar Al-Qurani mai girma na duniya wanda ya gudana a ƙasar Jordan na shekarar 2024. Maryam Ibrahim Ɗan'azumi ita ce gwarzuwar shekara a gasar Al-Qurani mai tsarki na ƙasa wanda ya gudana a jihar Kaduna na shekarar 2024 Dukkkaninsu mahaifinsu ɗaya daga jihar Gombe. Jama'a ku yi musu fatan alkhairi.