Jama'ar Garin Rigasa Sun Wulakanta Gawar Wakin Mutane Biyu (2) Da Hana Birnesu.
Wani mummunan al'amari ya faru a garin Kaduna!
wasu mutane da ba'a san ko su waye ba sun shiga maƙabartar layin bola dake
unguwar rigasa da wata motar asibiti (ambulance Car), Inda suka yi yunƙurin
birne wasu gawarwaki guda biyu ba tare da sanin hukumar maƙabartar ba.
Bayan
jama'ar gari sun sami labari shi ne suka je suka yo waje da gawarwakin da ba'a
san ko na su waye ba, da kuma dalilin da yasa aka kashesu ba, sannan suka
cinnawa motar asibitin wuta kamar dai yanda Kuke gani a a hotunan dake Kasa.
Zuwa
yanzu dai ba'a san dalilin da yasa akayi yunƙurin birne gawarwakin a sirrance
ba, kuma ba a san ko gawarwakin su waye ba, A taƙaice dai jama'ar gari sun
ɗauki doka a hanunsu,wanda wannan yunƙurin ɗaukar dokar ne yasa aka rasa
wadanda suka zo da gawar wakin, domin sun bi ta cikin Hayaniya sun sulale sun
gudu.
إرسال تعليق