Ana Wata Ga Wata: Mutanen Gaza Sama Da 440,000 Sun Gudu

Gaza: Mutum 450,000 Sun Tsere Daga Rafah Cikin Mako Ɗaya - MDD

Kimanin Falasɗinawa 450,000 ne suka tsere daga Rafah a cikin mako ɗaya da ya gabata, in ji Majalisar Ɗinkin Duniya, yayin da rahotanni ke cewa tankokin yaƙin Isra'ila na ci gaba da nausawa zuwa birnin da ke kudancin Gaza. Hukumar ayyuka da agaji ta MDD a yankin Falasɗinawa ta ce "al'umma na shan wahala kuma suna cikin yunwa da fargaba".

Sojojin Isra'ila sun ce suna ci gaba da "kakkaɓe cibiyoyin ƴan ta'adda" a gabashin birnin, inda sama da mutane miliyan ɗaya ke samun mafaka. Sabbin hare-haren da Isara'ila ta ƙaddamar a arewacin Gaza sun tarwatsa wasu mutanen kimanin 100,000. Dakarun Isra'ila sun sake ƙaddamar da farmaki kan yankin Jabalia Zeitoun, inda sojojin Isra'ila suka ce mayaƙan Hamas sun sake yin sansani, wata biyar bayan Isra'ilar ta bayar da rahoton cewa ta kakkaɓe bataliyoyin Hamas a yankin.

Sojojin Isra'ila sun buƙaci fararen hula su fice daga gabashin Rafah da Jabalia domin tsira da rayukansu gabanin ƙaddamar da hare-haren, sai dai yawan waɗanda aka sake tagayyarawa a yanzu ya kai kimanin ɗaya cikin huɗu na al'ummar Gaza, mutum miliyan 2.3. Isra'ila ta ƙaddamar da yaƙi kan Gaza ne domin kawar da Hamas a matsayin martani kan wani hari da aka kai mata a ranar 7 ga watan Oktoba, lamarin da ya yi sanadiyyar kashe mutane kimanin 1,200 tare da yin garkuwa da wasu mutanen guda 252.

Sama da mutum 35,170 ne aka kashe a Gaza tun daga wancan lokacin, kamar yadda ma'aikatar lafiya a yankin ta bayyana. A ranar Talata Hukumar ayyuka da bayar da agaji ta MDD ta wallafa hotuna titunan birnin Rafah waɗanda suka kasance fayau, amma titunan sun kasance maƙare da tantuna gabanin hare-haren da Isra'ila ta ƙaddamara a ranar Litinin.

Hukumar ta ce iyalai sun gudu domin neman mafaka, amma "Babu inda ke da aminci. Tagaita wuta nan take shi ne kawai mafita."

Ta yaya za a kwatanta ƙarfin Iran da na Isra'ila?

Shin daga ina Isra'ila ke samun makamai?

Halin da ake ciki a Gaza wata shida da fara yaƙi

Mai magana da yawun Unrwa, louise Wateridge wadda ke a Rafah, ta rubuta a shafinta na X cewa iyalan da suka saura a cikin birnin "sun matsa zuwa maƙurar birnin ta yamma" kuma sun kafa tantuna a bakin gaɓar tekun Meditaraniya. Cikin birnin a yanzu ya zama tamkar kufai".

Falasɗinawa kuwa sun faɗa wa kamfanin dillancin labaru na Reuters cewa tankokin yaƙi na nausawa zuwa cikin unguwanni a kudu maso gabashin Rafah kuma sun tsallake titin da ya tashi daga arewa zuwa kudanci, zuwa mashigar da ake tsallakwa zuwa Masar, wadda dakarun Isra'ila suka karɓe iko da ita a ranar Talata. Ɗaya daga cikin waɗanda suka yi magana ya ce "Tankokin yaƙin sun matsa zuwa titin Salah al-Din da safe, suka shiga unguwar al-Jneineh." "Suna nan a cikin unguwanni kuma ana ta fafatawa".

Hukumar tsaron Isra'ila ta IDF ta umarci mazauna su tashi daga unguwannin al-Jneinah da Brazil da wasu unguwanni da dama da ke gabashi a makon da ya gabata. An umarce su su koma "wasu matsugunai da aka samar". A wata sanarwa a ranar Talata, IDF ta ce dakarun Isra'ila sun "lalata maɓoyar ƴan ta'adda da dama a dab da mashigar Rafah ta ɓangaren Gaza", da kuma "kashe ƴan ta'adda da dama da gano makamai" a gabashin yankin Rafah.

Bayan kwashe wata bakwai ana yaƙi a Gaza, Isra'ila ta dage kai da fata cewa ba za ta cimma nasara ba har sai ta karɓe birnin Rafah tare da kawar da sauran bataliyoyin Hamas. Sai dai Majalisar Dinkin Duniya da ƙasashen yammacin duniya sun yi gargaɗi ƙaddamar da yaƙi kai-tsaye kan yankin zai haifar da kisan fararen hula da dama da kuma jefa mutane cikin bala'i.

Bugu da ƙari, ɗinbin Falasɗinawa da aka tarwatsawa a birnin, Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa man fetur, da abinci da abubuwan buƙatu ɗin da take bayarwa na gab da ƙarewa kasancewar an rufe mashigar Rafah da ta Karem Shalon. A ranar Litinin, Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe ɗaya daga cikin ma'aikatanta yayin da aka raunata wani a lokacin da suke tafiya zuwa wani asibiti da ke birnin Khan Younis, a arewa maso gabashin Rafah.

Post a Comment

Previous Post Next Post