Yanzu-yanzu: Gwamnati Ta Dakatar Da Harajin Tsaron Intanet

Yanzu-yanzu: Gwamnati Ta Dakatar Da Harajin Tsaron Intanet Kan Hada-hadar Kudade

Gwamnatin tarayya ta dakatar da zabge kaso 0.5 cikin 10 na hada-hadar kudi da aka yi a yanar gizo domin biyan harajin tsaro na yanar gizo. Ministan yada labarai da wayar da kai, Mohammed Idris ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a ranar Talata bayan kammala taron kwanaki biyu na majalisar zartarwa ta tarayya da shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a fadar shugaban kasa.

Yanzu-yanzu: Gwamnati Ta Dakatar Cire Kaso 0.5 Na Tsaron Yanar Gizo Kan Hada-hadar Kudade Tsaron Yanar Gizo: TUC Ta Yi Barazanar Shiga Zanga-zanga A Nijeriya, A cewar sa, ana kan sake duba harajin amma yanzu dai, an dakatar da shirin.

Idan ba a manta ba, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayar da umarni ga dukkan bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi, inda ya umarci a aiwatar da zabge harajin kaso 0.5 cikin 100 na tsaron yanar gizo kan duk wata hada-hadar kudi ta yanar gizo.

 Sai dai, wannan umurni ya gamu da suka da turjiya ta bangare da dama, tun daga kungiyoyin kwadago, ‘yan kasuwa, da jama’a saboda fargabar cewa, hakan na iya kara jefa ‘yan Nijeriya cikin mawuyacin hali baya ga tabarbarewar tattalin arzikin da suke ciki.

Post a Comment

Previous Post Next Post