Da Dumi-Dumi: Findi George Ya fara Aiki A Matsayin Sabon Mai horas Da 'Yan wasa

 Finidi George Ya Fara Aiki A Matsayin Sabon Mai Horos Da ‘Yan Wasan Super Eagles Ta Nijeriya.

Ministan wasanni, John Enoh, ya kaddamar da tsohon dan wasan Nijeriya, Finidi George, a  matsayin babban kociyan tawagar kwallon kafa ta Super Eagles a ranar Litinin a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja. Sabon Kociyan Kungiyar Kwallon Kafa ta Super Eagles, Finidi George, yayin da yake fara aiki a yau Litinin a Abuja.

Sabon Kociyan Kungiyar Kwallon Kafa ta Super Eagles, Finidi George, yayin da yake fara aiki a yau Litinin a Abuja Sabon kocin na Super Eagles ya kuma zabi tsohon abokin wasansa na kasa, Daniel Amokachi da wasu ‘yan kasashen waje biyu a matsayin mataimakansa, Finidi ya bayyana hakan ne bayan bayyana shi ga manema labarai a hukumance a matsayin sabon koci a Abuja.

NFF Za Ta Gabatar Da Finidi George A Matsayinl Sabon Kocin Super Eagles A Yau Litinin

Kalubalen Da Ke Gaban Finidi George, Har ila yau ya kuma kuma bayyana Olatunji Baruwa a matsayin mai horar da masu tsaron ragar tawagar, Baruwa dai shi ne ya rike mukamin a karkashin tsohon kocin tawagar Jose Peseiro.

Tsohon dan wasan na Ajax mai shekaru 53, kuma tsohon kocin Enyimba Finidi ya ce babban burinsa shi ne ya lashe wasanni biyu na neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za su kara da Afirka ta Kudu da Jamhuriyar Benin. 

Ya yi kira ga kafafen yada labarai da su ba shi goyon baya, yana mai cewa aikin ba abu ne mai sauki ba, ina so na roke ku a matsayinku na kafafen yada labarai cewa muna bukatar goyon bayanku, don Allah.

Labarai Masu Nasaba

Obi Na Jam’iyyar Labour Ya Yi Wata Ganawar Sirri Da Tsohon Gwamnan Jigawa Sule Lamido

NLC Na Gudanar Da Zanga-zanga A Ofishin KEDCO Na Kano Kan Ƙarin Ƙuɗin Wutar Lantarki

 Kafin yanzu Finidi ya kasance mataimaki ga Peseiro a gasar cin kofin Afrika na karshe da aka kammala a Ivory Coast, inda Nijeriya ta kare a matsayi na biyu.

Post a Comment

أحدث أقدم