Da Dumi-Dumi: Sarki Charles Na Burtaniya Ya Mika Mukaminsa Ga Ɗansa Bisa Wasu Dalilai

Sarki Charles Na Birtaniya Ya Miƙa Muƙaminsa Na Babban Jami'in Soji Ga Ɗansa Yarima William Mai Jiran Gado A Wani Biki Da Aka Gudanar.

"Babban abin shi ne ya kasance ya iya tuƙin jirgi," in ji Sarki Charles. Ba kasafai aka cika ganin Sarki da yariman Wales wuri ɗaya a taro ba - kuma wannan ya kasance wata babbar alama ta miƙa ragamar. Sarkin ya kasance babban jami'in soji tsawon shekara 32 kuma a yanzu, babban ɗansa Yarima William ya gaje shi.

Sarkin ya gana da Yarima William a bikin ba shi muƙamin na soji, bayan da ya sauka daga helikwafta a Hampshire. A wani jawabi da ya yi, Sarkin ya ce ya miƙa ragamar ne "cike da rashin jin daɗi bayan shekara 32 da sanin dukkanku". Ya yi magana kan sha'awar da yake da ita ga aikin rundunar sojin sama a Iraq da Afghanistan sannan ya zaɓi babban ɗansa kuma magajinsa.

"Ina fatan za ku ci gaba da samun nasara a nan gaba tare da Yariman Wales a matsayin shugabanku. Babban abin shi ne ya iya tuƙa jirgi. Don haka abin ƙwarin gwiwa ne," in ji Sarki.

Mene ne aikin Sarkin Ingila kuma su wane ne 'ya'yan sarautar?

3 Mayu 2023 .Sarki Charles III na Birtaniya na fama da cutar kansa

6 Fabrairu 2024

Yadda rashin lafiyar Sarki Charles III za ta shafi yarima William da Harry

6 Fabrairu 2024

Yarima William wanda yake matuƙin jirgin agaji na RAF, ya shafe shekara uku a sansanin sojin sama na RAF Valley da ke Anglesey. Sarkin bai ambaci ƙanin Yarima William ba wato Harry, wanda ya taba aiki sau biyu a Afghanistan. Sannan kuma Yarima Harry bai gana da Sarki ba lokacin da ya je Birtaniya a makon da ya gabata, inda kakakin Harry ya ce sarkin na da ayyuka da dama a gabansa.

Daga nan Yarima Harry da maiɗakinsa Meghan suka kai ziyara Najeriya tare da halartar taruka da suka shafi wasan Invictus da ake shirya wa ƴan mazan jiya da sojojin da suka ji rauni a fagen daga. Bayan da Sarki Charles ya bar wajen bikin miƙa ragamar, Yarima William ya gudanar da aikin karon farko a sabon muƙaminsa - ya samu ƙarin haske kan ayyukan rundunar sojin sama ta Birtaniya.

Post a Comment

أحدث أقدم