Da Dumi-Dumi: Tsohon Gwamnan Kogi Yahayya Bello Zai Gabatar Da kansa A Gaban Kotun.

 

Tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello Zai Gabatar Da Kansa A Gaban Kotu Ranar 13 Ga Watan Yuni


Tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello Zai Gabatar Da Kansa A Gaban Kotu Ranar 13 Ga Watan Yuni
Bayan kai ruwa rana, daga karshe dai tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya amince ya mika kansa a gaban kotun tarayya da ke Abuja a ranar 13 ga watan Yuni kan tuhume-tuhumen da hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) take yi masa kan almundahanar makudan kudade.


Lauyan da ke tsayawa, Yahaya Bello, Abdulwahab Mohammed, ya yi wa mai shari’a Emeka Nwite, alkawari a ranar Juma’a, bayan kotun ta ki amincewa da bukatar dakatar da shari’ar da wanda ake kara ke yi.

Zargin Badakala: Tataburzar EFCC Da Yahaya Bello Na Daukar Sabon Salo, Zan Yi Murabus Matukar Ba A Gurfanar Da Yahaya Bello Ba Shugaban EFCC. Muhammad ya ce tsohon gwamnan baya tsoron a gurfanar a gaban kotu ko kadan.



Lauyan tsohon gwamnan ya shaida wa kotun cewa, rayuwar wanda yake karewa na fuskantar barazana a Abuja, don haka ya yanke shawarar buya don tsira da rayuwarsa. Alkalin ya ce Bello ba shi ne tsohon gwamna na farko da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta gayyace shi kadai ba, kuma ba zai zama na karshe ba.

Labarai Masu Nasaba
Sabon Shirin Auren Zawarawan Kano A Sikeli
Yaushe Za A Kawo Karshen Karancin Man Fetur?
 


Alkalin kotun ya kuma ce ana tuhumarsa ne kan zargin da ba a tabbatar da shi ba, inda ya kara da cewa doka ma tana daukar duk wanda ake tuhuma ba shi da laifi har sai an tabbatar da laifin. A karshe dai Mai shari’a Nwite ya sanar da ranar 13 ga watan Yuni don Yahaya Bello ya gurfana a gaban kotu domin fara sauraran kara.

Post a Comment

Previous Post Next Post