Da Dumi-Dumi: Tsare "Daniel Ojukwu" Barazana Ne Ga 'Yancin Aikin Jarida A Nigeria

Tsare Daniel Ojukwu Barazana Ne Ga Ƴancin Aikin Jarida A Najeriya  HRW

Ƙungiyar kare haƙƙin bil adama ta Human Rights Watch ta ce tsare ɗan jaridar nan a Najeriya, Daniel Ojukwu ya take ƴancinsa a matsayin mai bayar da rahoto.


Ƙungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar wadda ta aike wa kafafen yaɗa labarai a Najeriya. HRW ta nemi hukumomin Najeriya su gaggauta sakin Ojukwu idan ba a tuhume shi da aikata babban laifi ba. A cewar ƙungiyar, ƴan jarida da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil adama a Najeriya na zanga-zanga kan kama Daniel Ojukwu tare da tsare shi.


Ɗan jaridar da ke aiki a gidauniyar aikin jarida na bin diddigi, ya ɓata ne a ranar 1 ga watan Mayu. Daga bisani kuma an gano cewa yana hannun ƴan sanda, inda aka zarge shi da take dokar yaƙi da laifukan intanet ta Najeriya. Ƙungiyar ta ƙara da cewa hukumomi sun yi ta watangaririya da shi a tsakanin ofisoshin ƴan sanda har da cibiyar daƙile laifukan intanet da sashen binciken manyan laifuka a Abuja.


HWR ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ta yi tanadi cewa duk wanda ake zargi da aikata laifi a gurfanar da shi a gaban kotu cikin sa'a 48 da aka kama shi. Ƙungiyar ta ce "Ojukwu ya ci gaba da zama a tsare ba tare da tuhumarsa ba fiye da kwana tara."


Wurin aikin Ojukwu ya ce an kama ɗan jaridar ne kan wani rahoto da ya yi wanda aka wallafa a watan Nuwamba, inda ya zargi wani tsohon babban mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan shirin tabbatar da muradun ƙarni, Adejoke Orelope-Adefulire, da tura naira miliyan 147 na asusun gwamnati domin gina makarantu zuwa wani asusun banki na gidan abinci.

Post a Comment

Previous Post Next Post